✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara hako man fetur a jihar Kebbi -Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya ce kwanan jihar za ta zama daya daga cikin jihohin da ake hako man fetur a Najeriya, inda…

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya ce kwanan jihar za ta zama daya daga cikin jihohin da ake hako man fetur a Najeriya, inda za ta bi sahun sauran jihohin da ake samar da man fetur ta hanyar hadingwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Hukumar Kula da albarkatun Man Fetur ta Kasa NNPC.

Gwamnan ya kara da cewa, ”A yanzu haka mun yi hadingwiwa da kamfanin Jamus don samar  da abubuwan more rayuwa. Kwanan za a kaddamar da kamfanin sarrafa tumatiri a jihar da kamfanin shinkafa kamar su: WACOT, LABANA da Dangote, yayin wasu kamfanonin da suke garuruwan Kamba da Yauri ke ci gaba da rubanya abin da suke sarrafawa“.