✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara noman Dankalin Turawa a Jihar Katsina – Shugaban Manoma ta AFAN

Nan gaba kadan za a  fara noman Dankalin Turawa da kawo sauran dabarun noman rani da na damina a Jihar Katsina. Shugaban Ƙungiyar Manoma ta…

Nan gaba kadan za a  fara noman Dankalin Turawa da kawo sauran dabarun noman rani da na damina a Jihar Katsina.

Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (AFAN), reshen Jihar Katsina kuma tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ne ya shaida wa wakilin Aminiya haka, jim kaɗan bayan ƙaddamar da sababbin shugabannin da za su jagoranci kungiyar a farkon makon nan. “Aikin kungiya ce ta faɗakar da manoma ta hanyar fiddo da wasu abubuwa masu muhimmanci don anfanin mambobinta. Don haka, noman Dankalin Turawa na daga cikin abubuwan da za mu mayar da hankali a kai, ba sai an je Jihar Filato ko Kaduna ba. Allah Ya albarkaci Jihar Katsina da kasa wadda duk abin da aka shuka a cikinta zai fito ya yi amfani. Ba  noman Dankalin Turawa ba hatta noman rani za mu sake masa fasali domin tafiya da zamani. Kada a cakuɗe waje ɗaya, za mu yi lura da shiyya da kuma wuraren da ake noman ranin domin ɓullo da hanyoyin da za su sanya amfanin kowane yanki ya zamo mai daraja ta yadda manomi zai ci gajiyar abin da ya noma sosai da kuma ƙara samun kudaden shiga. Saboda haka, yana da kyau a sani cewa, kara wa Jihar Katsina kasar noma ta kowace fuska yanzu, jarrabawa ce ke ba mu yi,  amma da mun ɗauko wannan mataki, Allah kuma zai taimake mu mu ga mun kai ga nasara,” inji shi. Alhaji Ya’u Gwajo-Gwajo ya ce, babban dai abin da za su kula da shi,  shi ne, manomi ya samu ingantaccen iri da  maganin ƙwari, domin kowane irin tsiro yana tare da wani sinadarin da zai janyo masa ƙwari. Saboda haka, yana da kyau manoma su riƙa sanin irin waɗannan dabarun noma domin za su ƙara kawo musu kuɗaɗen shiga.

Da ya juya kan batun noman shinkafa da rogo da riɗi da sauransu, Shugaban ya ce, yanzu manoman sun shaida su da kansu. “A je wajen su Ɗandume da wannan yankin a ga  irin shinkafar da ake nomawa. Riɗi da rogo ko’ina ka shiga a cikin jihar  babu inda ba a yi. In taƙaita maka a yanzu muna shirye-shiryen ganin cewa duk wani amfanin gona da ake gani sai da damina kawai ake shuka shi za mu riƙa noma shi sau biyu a shekara, wato rani da damina. Misali, wake da masara da gyaɗa da sauransu. Kuma nomansu a ranin zai fi kawo riba. Sannan kamar yadda na fada maka a baya, ƙungiya na nan tana neman sababbin hanyoyin noman zamani don amfanar da manoma,” inji shi.

Da ya juya kan ci gaba da harkokin ƙungiyar a tsakanin mambobinta, Alhaji Ya’u Gwajo-Gwajo, ya yi kira gare su cewa, su  ci gaba da bai wa ƙungiyar haɗin kai don ganin ta cimma burin kafata. “Akwai hanyoyi da yawa da gwamnati ke shigowa don bayar da tallafi, amma sai dai mu ji an samu wadansu sun zagaye sun karɓi miliyoyin kuɗi da sunanmu. Hakan yana faruwa ne saboda rashin haɗin kai. Sannan babban abin da ke da muhimmanci ga kowace ƙungiya shi ne, samar da kudaɗen shiga. A nan ina so in yi ƙara jan hankalinmu baki ɗaya a kan bayar da tallafin kuɗaɗen shiga. Da kudaden ne duk wani abin da ya taso za mu yi saurin ɗaukar mataki a kai ba sai mun tsaya raɓe-raɓe ba. Saboda haka, yanzu ƙalubale gare mu wajen ganin mun ciyar da ƙungiyar gaba.

Shi kuwa Alhaji M. T. Bello, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ta Ƙasa mai kula da Shiyyar Arewa maso Yamma wanda ya wakilci Shugabanta na kasa a wajen ƙaddamar da shugabannin ya ce, akwai rassan ƙungiyar a ko’ina a fadin ƙasar nan domin bayar da kowace irin gudunmawa ga manoma. Ya ƙara da cewa, yadda wannan gwamnati ta Shugaba Buhari ta bayar da muhimmanci  kan harkar noma inda ta ɗauki mataki kan samar da ingantaccen iri don bayarwa ga manoma, kuma take daƙile shirin ɓatagari da ake samu a wannan fanni abin yabo ne.

Da ya juya kan batun wuraren da ba za su iya noma ba saboda matsalolin tsaro, Mataimakin Shugaban ya ce, gwamnati na ƙoƙarin ganin cewa an samar musu da wuraren da za su yi noma kuma ƙungiya ce za ta yi ƙoƙarin ganin hakan ya samu. “Kazalika, gwamnati na wani shiri na kafa wata ma’ajiyar kayan abinci domin ƙaurace wa asarar da manoman ke samu sanadiyar hare-hare da ƙona musu kayan abinci. Manomi zai ɗebi kayan abincin da yake bukata saura kuma ya kai waccan ma’ajiya inda za a rubuta irin kayan da ya kawo a kuma ba shi takardar shaida. Hatta da bashin banki in manomi na bukata, zai je da wannan takarda a bankin bayan sun tabbatar daga wajen ma’ajiyar, za su ba manomin bashin, amma na rabin kuɗin abin da ya ajiye. In kuma amfanin gonar ya samu tagomashi wajen farashi, za a tuntubi  manomi in yana bukatar a sayar masa, in an sayar za su ɗauki kamishonsu su ba shi sauran kuɗinsa,” inji shi. Ya ce,wannan tsari zai taimaka matuƙa, kuma bai tsaya a kan waɗanda aka kora ba, kowane manomi yana iya shiga cikin tsarin.

Alhaji M. T. Bello ya yi kira ga shugabannin da aka ƙaddamar cewa, su ji tsoron Allah, su tsare gaskiya da riƙon amana.

Daga cikin shugabannin da aka kaddamar akwai Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo a matsayin Shugaba da Mataimakinsa Alhaji Abdulƙadir Nasir, sai Mataimaki a ɓangaren samar da kayan amfanin gona ta fuskar tsirrai, Alhaji Muntari Lawal. Sauran sun haɗa da Dokta Lawal Usman Bagiwa a matsayin Mataimaki ta fuskar dabbobi, sai na sashen itatuwa, Alhaji Farouk Lawal Joɓe. Kujerar Sakataren Ƙungiyar ta faɗa hannun Alhaji Bala Sani, yayin da Alhaji Halilu Ibrahim ya zama Ma’aji. Su kuwa Barista Abubakar Mukhtar da Hajiya Binta Haruna Dalhatu su ke wakiltar matasa da mata da sauran shugabanni. Alhaji Dahiru Mangal da Alhaji Abdullahi Imam Musawa da kuma Alhaji Lawal Idi Bagiwa su ne iyayen ƙungiyar.