✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara shari’ar Jami’an Hukumar NFF a ranar 1 ga watan Yuli

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ware ranar 1 ga watan Yulin 2019 a matsayin ranar da za ta fara sauraron karar da aka…

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ware ranar 1 ga watan Yulin 2019 a matsayin ranar da za ta fara sauraron karar da aka kai manyan jami’an hukumar NFF su biyar.

Manyan jami’an NFF da ake tuhumar sun hada da shugabanta Mista Amaju Pinnick da Janaral Sakatare Muhammed Sanusi da Mataimakin Shugaban Hukumar Na daya Oluseyi Akinwumi da Mataimakin Shugaban Hukumar Na biyu Shehu Dikko da kuma memba a babban kwamitin hukumar Ahmed Yusuf Fresh.

Ana zargin wadannan jami’ai ne da aikata laifuffuka 17.  Daga cikin laifin da ake zargin jami’an sun aikata akwai  karkatar da Dala Miliyan 8 da dubu 400 kimanin Naira Biliyan 3 da Miliyan 600 da Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta ba Najeriya saboda halartar gasar cin kofin duniya a 2014.

Sannan akwai zargin da ake musu na sayar da kadarorin hukumar da aka kiyasta a kan Naira biliyan biyu ba bisa ka’ida ba.  Haka kuma ana zarginsu da kin bayyana kadarorin da suka mallaka ga Kwamitin da shugaban kasa ya kafa na kwato kadarorin gwamnati daga hannun wadanda suka wawure (SPIP).

Wadannan da wasu dalilai ne suka sanya Alkalin kotun Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ya ba Kwamitin shugaban kasa na kwato kadarorin gwamnati damar gayyato jami’an na NFF don su halarci zaman kotun a ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa don fara sauraron kara a kansu.

Tun da farko Lauyan Kwamitin SPIP Celsius Ukpong ya koka ne a game da yadda kwamitin ya rika aika takardun gayyata ga jami’an a lokuta daban-daban amma suka ki amsa gayyatar.

Idan ba a manta ba, tun a 2014 ake zargin shugabannin hukumar da laifin karkatar da makudan kudin da FIFA ta ba kungiyar Super Eagles saboda halartar gasar cin kofin duniya.