✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fassara dokokin wasanni cikin harshen Hausa

A kokarinta na magance tashe-tashen hankulan da ke faruwa a dalilin wasanni a fadin Jihar Kano, gwamnatin jihar ta ce za ta fassara ka’idojin wasannin…

A kokarinta na magance tashe-tashen hankulan da ke faruwa a dalilin wasanni a fadin Jihar Kano, gwamnatin jihar ta ce za ta fassara ka’idojin wasannin kwallon kafa da kuma na kungiyoyin wasanni na kasa (rules of soccer and those of the Nigerian Premier Football League)cikin harshen Hausa.

Gwamann Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ne ya bayyana haka a lokacin da yake rattaba hannu akan wata takardar yarjejeniya da aka kulla tsakanin gwamnatin da kungiyar wasa ta Masita sport, da ke kasar Holland da kuma takwararta ta Elite Sports Consulting, da ke Amurka.
A cikin kunshin wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan Watsa Labarai na Gwamnan Halilu Ibrahim dantiye, Gwamna Kwankwaso ya shawarci ma’aikatun da ke kula da wasannin kwallon kafa a fadin kasar nan da su fassara dokokin da ka’idojin da suka shafi wasannin zuwa harasan cikin gida don amfanin masu sha’awar wasannin a fadin kasar nan.
Kwankwaso ya ce “Abin damuwa ne kwarai yadda magoya bayan masu buga wasannin kwallon kafa ke amfani da damar lokutan ire-iren wadannan wasanni suna haifar da fitina. Saboda haka ba za mu yarda da duk wani abu da zai kai ga faruwar tashin hankali ba” Inji Gwamannn Haka kuma Gwaman ya kara da cewa “Gwamanatin Jihar ta yi alkawarin sake bibiyar dukkanin tsofoffin dokokin da tsare-tsaren wasanni a jihar ta yadda zai yi daidai da na sauran kasashe a duniya musamman abin da ya shafi yaki da cin hanci da rashawa a bangren wasanni da kuma kokarin samar da ‘yan wasan tare da kula da walwalarsu domin jihar ta zama kan gaba a fagen wasanni.” Inji shi.
A nasu jawaban daban-daban, wakilin kungiyar wasanni ta Masita sports ta kasar Holland Mista Taled Radloff da takwaransa na kungiyat Elite Sports Consulting, da ke Amurka Mista Tama Aondofar, sun yi alkawarin aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma cikin nasara.

 

Jadawalin Gasar Rukunin Premier Na Ingila A Wannan Mako:
Asabar 9 Ga Nuwamba, 2013

Aston billa da Cardiff City Hudu na yamma
Chelsea da West Bromwich Albion Hudu na yamma
Crystal Palace da Eberton Hudu na yamma
Liberpool da Fulham Hudu na yamma
Southampton da Hull City Hudu na yamma
Norwich City da West Ham United Shida da rabi

Lahadi 10 Ga Nuwamba, 2013
Tottenham Hotspur da Newcastle United daya na rana
Sunderland da Manchester City Uku da minti biyar na rana
Manchester United da Arsenal Biyar da minti 10 na yamma
Swansea City da Stoke City Biyar da minti 10 na yamma

Jadawalin Gasar La-Liga Ta Sifen A Wannan Mako:
Juma’a 8 Ga Nuwamba, 2013

Osasuna da Almeria Takwas na dare
Granada da Malaga Goma na dare

Asabar 9 Ga Nuwamba, 2013
Real Madrid da Real Sociedad Hudu na yamma
Getafe da Elche Entradas Shida na yamma
Athletic Bilbao da Lebante Takwas na dare
Celta bigo da Rayo ballecano Goma na dare

Lahadi 10 Ga Nuwamba, 2013
Espanyol da Sebilla FC Sha biyu na rana
balencia da Real balladolid Biyar na yamma
billarreal da Atletico Madrid Bakwai na dare
Real Betis da Barcelona Tara na dare