✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fitar da ’yan takarar zabukan Majisar kasa da kananan hukumomi a Kamaru

Jam’iyyar RDPC mai mulki da babbar Jam’iyyar ‘yan adawa wato SDF za su gabatar da ‘yan takara a duk mazadun kasa. Hukumar zabeta kasar Kamaru,…

Jam’iyyar RDPC mai mulki da babbar Jam’iyyar ‘yan adawa wato SDF za su gabatar da ‘yan takara a duk mazadun kasa. Hukumar zabeta kasar Kamaru, wato ELECAM na tantance ’yan takara Sauran jam’iyyun kuwa, sun ta’allaka ne ga neman goyon bayan masu kada kuri’a a yankin shugabannin jam’iyunsu. Wadannan jam’iyyun sun hada da UDC da  FSNC da UPC. Kowace jam’iyya dai ta jira karshen lokaci domin ta gabatar da takardun ‘yan takarta. Adadin kujerun da ake takara nan ‘yan majalisar dokoki 180 ne a yayin da kuma kansaloli kusan 10,000 ne ake bukata a duk fadin kasa. Dalilai kuma da dama ne suka sa aka samu rashin mika takardun ‘yan takara tunda farko ga Hukumar shirya zabe, Mataimakin mai kula da sadarwa a jam’iyar UNDP cewa ya yi.”UNDP ta kimtsa, “wasu takardun da za a gabatar ne suka kawo mana dan jinkiri wurin kammala jerin sunayen ‘yan takaran wasu mazabu”.
Jam’iyyar SDF  a shirye take, amma kuma akwai dan wani aikin da ya rage, abin da Alhadji Talle Ibrahim ya tabbatar ke nan.Ya ce suna ta binciken ingancin takardun ‘yan takararsu daya bayan daya. Saboda haka suka kafa kwamitoci da dama wadanda suke tafiyar da aiki tukuru gabanin wa’adin karshe”. Daga Sashen uwar jam’iyyu kuwa, wato RDPC mai rike da akalar mulki, inda a nan ba zaben fidda gwani ake yi ba, da alamun akwai rikice-rikice da suka dabaibaye tsaida ‘yan takara. Ga irin korafin da wani dan takara ya yi. “Jerin kundin sunaye daban-daban biyu muke da shi a birnin Limbe sai ga shi a nan kuma an ce da mu daya ne kawai. Ana nuna mana cewa babu wata matsala, alhalin kuma babban rikici ne ke kwance a Limbe”. Su kuma masu fada a ji a cikin jam’iyyar kamar mataimakain Sakatare janar, wato Gregoire Owona ba da tabbaci ya yi kamar haka.”Babu wani tashin hankali a cikin jam’iyyar mu, za mu kimtsa komai a lokaci, a yanzu haka tafiya muke yi da lokaci. Kuma za mu nemi hanyoyin masalaha game da irin kura-kuran da za mu gano. Za mu gabatar da shawarwari ga Sakataren jam’iyya. Ya rage kuma ga shi ya zartar da hukuncin da ya ga shi ne mafi dacewa”.
Ranar laraba 17 ga watan Yuli ce ta kasance karshen wa’adin karbar takardun tsayawa takara a tagwayen zabubbukan ‘yan Majalisar dokoki da kuma na kananan Hukumomi. Zabukan za a gudar da su a ranar 30 ga watan Satumbar bana. Bisa ga yadda doka ta tsara ko wani dan takara na da wa’adin kwanaki 15 daga ranar da aka tsayar da ranar zabe da ya bayyana manufarsa.
Shugaban kasa Paul Biya ya sa hannu akan dokar tsayar da ranar zabe, biyu ga Talatar wannan wata. Tun wannan lokacinne kuma jam’iyyun siyasa suka fada cikin shirye-shiyen karshe, domin ganin sun yi la’akari da doka wurin tsayar da ‘yan takara.