Search
Subscribe
Za a hana gwamnoni taba kudaden kananan hukumomi

Za a hana gwamnoni taba kudaden kananan hukumomi

Sashin Kula da Hada-Hadar Kudade na Sirri ya bai wa bankuna umarnin hana gwamnatocin jihohi taba kudaden asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi, har sai kudaden sun isa ga hannun kananan hukumomin

Aminiya ta gano cewa, wannan hani ga gwamnonin kan taba asusun kananan hukumomin zai shafi akasarin jihohin kasar nan .A sanarwar da mukaddashin shugaban sashin, Malam Ahmed Dikko ya fitar ta ce daga ranar 1 ga watan Yunin bana, duk bankin da ya karya wannan doka za a sa masa takunkumi a cikin da kuma wajen kasar nan.

Sashin ya ce za a bullo da sabbabbin ka’idoji da za su rage yawaitar laifuffukan almundahanar kudi da ake yi a kananan hukumomin kasar nan, kuma a sanar da hukumomin irin su Babban Bankin Najeriya da hukumomin EFCC da ICPC, cewa asusun hadin gwiwar jihohi da kananan hukumomi yana nufin asusun ne, na gamayya wanda duk ajiyar da ke cikinsa na zama tamkar rance ne ga karamar hukuma daga jiha, wanda za a yi amfani da shi ga kananan hukumomin jihar kawai, ba ga wasu ayyuka daban ba.

Cire kudade da hada-hada a wannan asusu da jihohi ke yi, ya kawo babban gibi da cin hanci da rashawa da kuma barazanar tsaro a yankunan karkara, sakamakon yadda gwamnonin jihohi suke karkatar da kudaden kananan hukumomin zuwa bukatun kansu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin