✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a hana tsoffin ‘yan INEC shiga siyasa

Majalisar Wakilai ta kammala karatu na farko a kan dokar hana tsoffin ma’aikatan hukumar zabe ta kasa (INEC) shiga siyasa sai sun shekara biyar da…

Majalisar Wakilai ta kammala karatu na farko a kan dokar hana tsoffin ma’aikatan hukumar zabe ta kasa (INEC) shiga siyasa sai sun shekara biyar da barin aikin.

Da yake gabatar da kudurin, Honarabul Olawale Raji ya ce hana jami’an INEC shiga siyasa nan take bayan sun bar hukumar zai kara wa ’yan Najeriya nutsuwa da harkar zabe da kuma hukumar.

Hana jami’an tsoffin INEC shiga siyasa da zarar sun bar aikin mai muhimmanci zai hana ma’aikatan hukumar yin amfani ko mukamansu wajen yi wa kansu shimfani a siyasance.

Wannan na daga cikin sauye-sauyen da majalisar ke kokarin yi ga dokar zabe ta Najeriya ta shekarar 2010.

Zaman Majalisar na ranar Talata ya amince da kudurin dokar domin yin karatu na biyu a kansa.