Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Za a haska fim din Kannywood a Amurka

Za a haska fim din Kannywood a Amurka

Mashirin fim din Jalil ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin haska kayataccen fim dinsu mai suna Jalil a Jihar Atlanta da ke Arewacin Amurka.

Jarumi Yakubu Mohammed, wanda ke daya daga cikin jaruman fim din ne ya bayyana haka a shafinsa na Instagram.

 

Yakubu Mohammed wanda ake kira da Yakx ya ce, “Za a kaddamar da fim din Jalil a Plaza Theatre da ke Atlanta a ranar 22 ga watan Maris. Wannan ne karo na farko da za a kaddamar tare da haska fim din Kannywood a Arewacin Amurka.”

Shi ma mashiryin fim din, Lesli No’iless Dapwatda, wanda mashiryin fim ne a Amurka ya bayyana cewa ya ji dadin fim din, sannan ya bayyana godiyarsa ga jarumai da suka taka rawa a fim din irinsu Yakubu Mohammed da Maryam Booth da Ali Nuhu da sauransu.

“Wannan duk kokarinku ne. Ina fata za ku kasance tare da mu a Atlanata domon kallon fim din.” Kamfanin shirya fina-finai na Noless Studio da ke Atlanta ne ya dauki nauyin fim din ya zimmar bayyana al’adun Afirka.