✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a iya magance matsalar talauci a Najeriya idan …… -Sanata Maccido

Sanata Ahmed Maccido shi ne shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawan Najeriya, kuma daya daga cikin matasan ’yan siyasar Arewa masu kima. A tattaunawarsa…

Sanata Ahmed MaccixoSanata Ahmed Maccido shi ne shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawan Najeriya, kuma daya daga cikin matasan ’yan siyasar Arewa masu kima. A tattaunawarsa da ’yan jarida, cikin har da wakilinmu, Bashir Yahuza Malumfashi, Sanatan ya bayyana yadda za a magance matsalar talaucin da ya addabi jihohin Arewa da kasa baki daya. Ga yadda tattaunawar ta gudana:

A matsayinka na Shugaban Kwamitin Kula Da Kasafin Kudi Na Majalisar Dattawa, ya kake ganin zancen aiwatar da kasafin kudi daga Gwamnatin Tarayya?
Alhamudu lillah. Hakika, gaskiya idan ka duba kasafin kudi na bana, bai samu karbuwa ba. A shekarar da ta gabata suna maganar sun samu nasarar aiwatar da ayyuka na kasafin kudi har kusan kashi 50 bisa 100. Amma mun san ba haka ba, nasararsu za ta tsaya ne tsakanin kashi 30 zuwa 38 bisa 100. A bana gaskiya ba mu tsammanin zai fi haka, domin bayan kammala ayyukan da muka yi na kasafin kudi, kamin Shugaban kasa ya sanya hannu sai da
aka yi ja-in-ja, domin a nasu gani, aikin da Majalisa ta yi ba haka suke son shi ba. To, amma sun manta da aikin da suke kawowa da wanda muke yi. Ya dace a ce mun zauna mun shata hanyoyi wadanda ya dace a ce mun samu jituwa da su ba tare da an ji hayaniyar daga waje ba. Dangane da haka ya sanya aikin da suka kawo, muka yi aikin da ya dace, muka mayar musu da shi, ba ainihin abin da suke so ba. Wannan ne dalilin da ya sanya fadar Shugaban kasa ta sake kawo wani gyara ga aikin da a kayi.
Ke nan fadar Shugaban kasa ba ta ji dadin aikin naku ba?
Haka ne. Watau manufarmu, gaskiya ba mu so mu canza  aikin da aka yi ba, domin abin da muke a Majalisa, muna yi iya kokarin da muke yi, amma saboda yadda al’mari na mulki yake gudana, su ne ke gudanar da ayyuka. Aikinmu shi ne mu tsara da zana su zuwa gare su. Gwargwado abin da muka ga ba za su iya yi ba, a wannan shekarar muka gyara muka ba su, domin su aiwatar.
Yanzu ke nan kun kammala gyaran wannan kasafin kudin har kun ba su?
Haka Majalisa ta amince, mun gyara mun kuma ba Shugaban kasa. Akwai hanyar gyaran matsalar, domin daman gyara suke nema ga al’amari. Mun yi mun kuma ba su, ya rage gare su na aiwatar da ayyaukan domin ci gaban al’ummar wannan kasa.
Majalisa tana da hanyoyin da suka wajaba gare ta na tabbatar da lura da kasafin kudi, aiwatar da shi da kuma nasararsa, wadanda tsarin mulki ya bayar. Tsarin mulki ya ba mu ikon bin diddigi a kan aikin da ake yi mu duba shi.
Me yake jnyo ana fuskantar matsala wajen aiwatar da kasafin kudi, bayan amincewa da shi tsakanin Majalisa da fadar Shugaban kasa?
Gaskiya aikin gwamnati ya dade haka, don kuwa amfani da ka’idojin da ake kira ‘bureaucracy’ a cikin gwamnati. Sakamakon yadda ake cewar sai fayil ya bi tebur daban-daban, ma’ana ofis daban-daban kafin kai ga amincewa ta karshe a fara aiki. Ana iya rage wannna ko kuma gyara hakan domin samun sauri da sakamakon kirki ya karfafa, domin samun natsuwa da aiki cikin lokaci.
Ya kake ganin yanayin da kasar nan take ciki yanzu a fannin tattalin arziki da samar da kudade cikin jama’a da rarraba arziki ga ’yan kasa?
Hannun jama’a kam, na shaida ba kudi.
Kana nufin ke nan akwai talauci a Najeriya?
Akwai talauci sosai a Najeriya kam. Kowa ya san da haka, kowa yana da shaida dangane da wannan. Wannan kuma ya faru sakamakon yadda gwamnati take daukar aikin tafiyar da harkar kasuwanci a Najeriya. Ba don komi ba kuwa sai domin akwai abin da suke kira bunkasa hanyoyin tattalin arziki na saye da sayarwa da shiga da fita na kudade, wato ka bayar da kudinka a kan abin da kake so. Sai kuma na sha’anin tattalin arziki wanda yake na rubuce-rubuce ne, a kan abin da ya shafi harkokin waje.
A nan sai Gwamnatin Tarayya ta fi mayar da hankalinta ga abin da ya shafi tattalin arziki na waje maimakon abin halin da kasa take ciki. Wannan ne dalilin da ya sanya za ka ji ana zancen ‘GDP’ na kasa ya karu, ya kai wuri kaza amma kuma ga talaka a cikin kasa yana fama da wahala saboda gwamnati ta mayar da hankalinta ga huldar tattalin arziki na waje fiye da abin da ’yan kasar suke mu’amala da shi a cikin kasa na kwabo da sisi.
Wannan ne ya janyo matsalar talauci ke nan?
Sanadiyar hakan ne ya kara taimakawa ga kasa da ’yan kasa fadawa cikin talauci. Za ka ji labarai ana maganar tattalin arziki ya samu karuwa har ya daukaka amma kuma ba haka ba ne, domin shi talaka ya san ba haka ba ne. Bai samu abinci ba, yana cikin wahalar rayuwa, ga kuma tsadar kayayyaki. Ashe ke nan akwai bambaci tsakanin abin da suke duba da wanda talaka yake ciki. Haka ma babu wani dalili wanda Gwamnatin Tarayya za ta bayar, domin kuwa Najeriya tana da isassun kudade a ciki da wajen kasa kuma ka ga mun yi kasafin kudi a kan sayar da gangar fetur dala 75 amma yanzu ana sayar da ita a kan dala 100 ko fiye.
Ko ana iya gyaran wannna matsalar?
kwarai da gaske kuwa, ai ya dace su dawo su fuskanci wannan matsalar, domin sha’anin tattalin arzikin kasa da ya wuce daya, mussaman ma wanda ya shafi rayuwar al’ummar kasa, dole ne a daidaita su domin tafiya hannun riga.
Ya kake ganin matsalar talauci a Arewa?
Hakika talauci a Arewa kamar nan ne uwa uba, domin
kuwa abin ya fara zama na fitar hankali, wanda hakan na nuna kamar dai ba a son magance lamarin. Idan ka lura, kamar dai ba a son a nuna Arewar nan tana cikin Najeriya. Duk Masa’antunmu da tun farko aka lura suna
yin kasa da wadanda suka rufe, abin ya kara yin kasa. Kamfunan da ’yan shekaru biyu da suka wuce suna aiki, su ma yanzu an rufe su baki daya.
Kamfuna irin masu yin atamfa ko man shafawa ko kuma sabulu, duk sun durkushe saboda rashin kulawa da kuma ba su karfin gwiwa daga Gwamnati.
Ku Sanatoci ’yan Arewa, me kuke yi dangane da hakan?
Idan ka lura, muhimmin aikinmu shi ne tsara doka da bayar da shawara. Mu tabbatar da cewar dokar nan an aiwatar da ita. Ka ga kusan kashi 90 bisa 100 na dokokin da muka yi a Majalisa, ba a yi aiki da su ba, suna nan an jefa a kasan kafet dinsu. Hakika da an yi amfani da su da kuwa yanzu ba karamin ci gaba za a samu ba a Najeriya, musamman Arewa.
Wannan matsala ta talauci da rashin tsaro, ba ka ganin ta yi wa Arewa yawa, ga kuma lokaci na kara tafiya?
Ina shaida maka, idan har ana son a magance wannan matsalar, dole ne sai dukkanin shugabanin Arewa masu mulki da wadanda suke ba su bisa mulki, sun fito fili sun yi wa kansu fada na gaskiya, sun janye tsoro, son kai da kwadayi; domin ganin an tallafa wa wa wannan yankin ga fitar da shi ga wanna bala’in na talauci da rashin tsaro.
Kamar yaya kake nufi?
Arewa, Allah Ya albarkace ta da mutane masu ilmi da hikima da dubara da iya mulki. Wanna yankin shi ne na daya daga cikin dukkan sauran yankuna da Allah Ya ba al’umma iri-iri, masu manufofi na ci gaba da iya hakuri da juna amma kuma muka yi watsi da duk wadannan koyarwa da kuma janyo wa juna hassada da neman cin zarafi tsakaninmu. Shugabaninmu wadanda suke da rayuwa da lafiya a yanzu, su fitar da wani babban tafarki na hadin guiwa da juna a yankin, domin kawo karshen matsalar tsaro da talauci da jahilci; wadanda su ne muhimman ababen magancewa.
Idan har shugabani wadanda suke bisa mulki suka sanya gaskiya da tsoron Allah da lamarin da ya shafi jama’a, ka ga matasalr talauci za ta zama tarihi, domin Allah Ya albarkace mu da kasar noma da hanyoyin bunkasa sana’oin hannu da na zamani a cikin al’umma. Sai maganar tsaro, ba abin da ya janyo shi idan ba rashin hadin kai da fahimtar juna a tsakaninmu ba. Idan aka yaki talauci, rashin tsaro zai zama tarihi ga Arewa.
Wannan yana iya yiyuwa kuwa?
Hakika hakan zai samu idan dan Arewa ya fuskanci cewa bai da abin da ya fi masa Arewa. Ya fito fili ya janye son kai da kwadayi da kiyayya ta addini da kabilanci da kuma rashin tsoro a kan abin da yake son Arewa ta kasance. Muna da gwamnoni, muna da masu kudi, muna da masu ilmi, ga mu da Sanatoci da ’Yan Majalisar Wakilai. Duk wadanan mun fi kowanne yanki yawa da karfi a nan Arewa, to me zai hana mu hadu a wuri daya mu yi wa juna fada, mu fadi gaskiya a kan junanmu tare da amincewa mu ceto al’ummarmu. Kana ganin idan har muka fara aiwatar da hakan a tare, wani ko wasu za su iya samun galaba a kanmu?
Zancen talauci da mgance shi fa?
Muhimmin abin da za a iya yi a yanzu don magance matsalar talauci a Najeriya shi ne, yaki da almubazzaranci da kuma tallafa wa l’umma da hanyoyin bunkasa rayuwarsu da samar musu ainihin abin da ya dace su samu ga romon dimokaradiyya. Tallafa wa al’umma ta hanyar bunakasa ilmi, gina hanyoyi, inganta kasuwanci da kuma hanyoyin cinikayya tsakanin juna, samar da tsaro da kuma ababen more rayuwa nakwarai ga al’umma. Matasanmu suna cikin wahala, sakanamkon kammala karatu babu ayyuka, iyayensu na fama da matsalar biyan kudaden makaranta da kuma ciyarwa, ga matsalar yawaitar tashe-tashen hankali da fadace-fadace na ta’addanci da shan kwayoyi tsakanin matasa a cikin birane da kauyuka. Wadannan duk Arewa ta fi daukar rabo mai yawa a cikin kasa. Talaucin nan ana iya magance shi idan har ainahin su wadanda suke da shugabanci sun tsaya cewar da gaske suna neman magance shi domin ceto al’umma.
Wane irin ci gaba ka kawo a mazabarka ta Sakkwato Ta Tsakiya?
Muhimmin abin da ya dace a lura, ba rabon kudade ko kuma gina gidaje manya ko sayen manyan motoci da babura domin bangar siyasa ne ma’uanin ci gaba da samun nasarar siyasa ba. Kamar yadda mai girma Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko yake kokarin ganin ya samar da bunkasa ilmi a Jihar Sakkwato, shi ne gwagwargadon abin da nake ganin ya fi dacewa na mayar da hankali ga aiwatarwa da kuma bunkasa aikin gona da ci gaban mazabata.
Wace irin gudumuwa ka bayar ga mazabar taka?
A yanzu haka na samar da isassun na’ura mai kwakwalwa da aka rarraba domin makarantun gaba da firamare, domin inganta karatun fasahar kimiyya da kuma bai wa dalibai karfin gwiwa ga ilminsu. Haka ma na gina asibiti mai gado 60 a kasar Samalo da ke karamar Hukumar Mulkin Wamakko, domin amfanin marasa lafiya da taimaka wa Gwamnatin Jihar Sakkwato ga ayyukan bunkasa lafiya a yankin mazabata.
Sai kuma samar da ruwan sha na injunan tuka-tuka da kuma rijiyoyin burtsatse a dukkanin kananan hukumomi takwas na Jihar Sakkwato. Bayan ga nemo guraben aiki a waje, akwai tallafa wa dalibai da suke da matsalolin kayan karatu da kuma sayen takardun ci gaba na karatu, tare da samar da guraben karatu da biyan kudaden rajista da kuma bude ajujuwa na mussaman, tare da biyan malamai domin koyar da su hanyoyin rubuta jarrabawa na NECO da WAEC da sauran fannoni daban-daban. Har yanzu ana ci gaba da bayar da makudan kudade a matsayini tallafi ga iyaye da marayu da kuma marasa galihu, wadanda gidauniyar da na kafa take bayarwa. Kusan mutane da dama suna amfana da wannan kuma na ci gaba da aiwatar da hakan tare da ba su jari na sana’a da sayen takin zamani a rarraba musu kyauta, domin bunkasa aikin noma. Baki daya dai muna aiwatar da hakan ta hanyar kafa kwamiti na wasu amintattun dattawa da samari a unguwanni, mazabu da kuma kananan hukumomi ba tare da mun fitar waje ba, domin manufa shi ne a tallafa wa al’umma.
Mene ne kalubalenka ke nan?
Ba shakka muhimmin kalubalen da ke gabana shi ne na ga talauci ya rage a cikin al’ummarmu ta Jihar Sakkwato, haka ma Arewarmu da kasarmu baki daya. Na fi son na mayar da hankali ga lamarin ilmi da noma a matsayin muhimman hanyoyin bunkasa rayuwar al’umma.