Da Dumi Dumi

Za a kammala gyare-gyaren tsarin mulkin kasar nan kafin shekarar 2015 – Kayarda

dan Majalisar Wakilai daga mazabar Lere a Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Lawal Nuhu Kayarda ya ce za a kammala gyare-gyaren tsarin mulkin kasar nan kafin shekarar 2015.
Alhaji Ibrahim Kayarda ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce wannan aiki yana tafiya yadda ya kamata a Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa.
Ya ce yanzu abin da ya rage shi ne a samu daidaituwa a tsakanin bangaren wakilai da dattawa kan kowane bangare da ake son a yi wa gyare-gyaren a kundin tsarin mulkin.
Ya ce da zarar an gama wannan shi ke nan sai a tura wa majalisun dokoki na jihohi don neman amincewarsu. Ya ce idan aka samu kashi biyu bisa uku na majalisun dokoki na jihohi suka amince shi ke nan wannan gyaran kundin tsarin mulki ya tabbata.
Da yake magana kan aikin gyaran hanyar Kaduna zuwa Jos kuwa, Alhaji Ibrahim Lawal ya ce muna iyakar kokarinmu wajen ganin an sake saka aikin hanyar a cikin kasafin kudin badi.
Ya ce aikin gyaran hanyar an fara shi ne tun a shekarar 2009, kuma  sun yi iyakar kokarinsu a bana an sanya kudi masu yawa don a ci gaba da aikin, amma sai aka samu tangarda kwangilar aikin ta tsaya a wani wuri.

Share