✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe Naira miliyan 526  a shirin UBE a Jihar Oyo

Gwamnan Jihar Oyo, Mista Seyi Makinde ya amince da ware Naira miliyan 526 kan shirin bayar da ilimi kyauta ga makarantun firamare 2,500 da sakandare…

Gwamnan Jihar Oyo, Mista Seyi Makinde ya amince da ware Naira miliyan 526 kan shirin bayar da ilimi kyauta ga makarantun firamare 2,500 da sakandare 640 da za su ci moriyar shirin a zango na farko na shekarar karatu ta 2019 da 2020. An kebe Naira miliyan 400 ga makarantun sakandare yayin da aka tanadi Naira miliyan 126 ga makarantun firamare.

Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan, Mista Taiwo Adisa ne ya bayyana haka a takardar sanarwar da ya raba wa manema labarai a Ibadan a ranar Litinin da ta gabata. Gwamnatin Jihar ta umarci shugabannin makarantun su bude asusun ajiyar banki domin tura kudin da za su gudanar da wannan  aiki, inda tuni wadansu shugabannin makarantun firamare suka fara karbar nasu kason daga banki. Su ma dalibai dubu 400 na makarantun sakandare 640 suka fara cin moriyar Naira dubu daya ga dalibi a zangon karatu daya da za a kashe Naira biliyan daya  da miliyan 200 a shekara kamar yadda aka sanar.

Sanarwar ta ce, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ita ke da alhakin raba wa makarantun sakandare kudin yayin da Hukumar SUBEB za ta mika kudin makarantun firamare. “Ware wannan kudi yana cikin alkawarin da Gwamna Seyi Makinde, ya yi ne na shirin samar da ilimi kyauta a jihar,” inji sanarwar.

Gwamnatin ta nemi masu ruwa-da-tsaki a wannan shiri su tabbatar cewa, sun kashe kudin yadda ya dace domin gwamnati za ta binciki yadda suka yi amfani da kudin.

Haka gwamnatin ta gargadi shugabannin makarantun kan kada su kuskura su kyale wadansu mutane su yi amfani da su wajen yin zagon kasa ga wannan shiri na samar da ingantaccen ilimi kyauta ga makarantun firamare da sakandare a  jihar. “Gwamnati za ta sa kafar wando daya da duk wanda aka samu da yin zagon kasa musamman yin amfani da daliban makarantun domin cimma mummunan burinsa,” inji sanawar.