✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a nada ’ya’yan manyan sarakunan Oyo hudu a matsayin kwamishinoni

Ya’yan manyan sarakuna hudu na Jihar Oyo na cikin jerin sunayen mutum 12 da Gwamna Abiola Ajimobi ya mika wa Majalisar Dokokin ta jihar yana…

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar OyoYa’yan manyan sarakuna hudu na Jihar Oyo na cikin jerin sunayen mutum 12 da Gwamna Abiola Ajimobi ya mika wa Majalisar Dokokin ta jihar yana neman amincewarta domin nada su a mukaman kwamishinonin jihar.

A kwanakin baya ne Gwamna Ajimobi ya rushe Majalisar Zartarwar Jihar, kuma a jerin sunayen da ya mika ga majalisar a ranar Talatar da ta gabata, ya sake mika sunan tsofaffin kwamishinoni biyar don sake nada su a matsayin kwamishinonin.
Daga cikin ’ya’yan sarakunan da Gwamna Ajimobi ya mika don nada su kwamshinoni akwai ’yar Alaafin na Oyo, Gimbiya Adetutu Akhigbe Adeyemi da ’yar Soun na Ogbomoso Gimbiya Olufunke Oworu da Yarima Gbade Lana, dan Olubadan na Ibadan da kuma dan Sarkin Musulmin kasar Yarbawa Alhaji Faruk Umar Aresekola Alao.
A shekaranjiya Laraba ce kwamishinonin 12 masu jiran gado suka gabatar da kansu a gaban majalisar dokokin kamar yadda ta umarce su, inda kowanne ya bayyana kansa dauke da kwafe 40 na takardun kammala karatu da ayyuka da ya yi zuwa yanzu.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin 23 ga Satumban bana ne Gwamna Abiola Ajimobi, ya ba da sanarwar rushe majalisar zartarwa da ta kunshi kwamishinoni da manyan masu ba shi shawara da yake tare da su tun lokacin da ya haye karagar mulkin jihar. Da yake rusa majalisar a wancan lokaci, Gwamna Ajimobi ya ce, ya yi haka ne domin janyo sababbin jini da za su bayar da irin tasu gudunmawar ga ci gaban jihar ta Oyo.