Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Za a rage wa ’yan wasan Man United albashi

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskskajear

Daukacin ’yan kwallon Manchester United da ke Ingila suna fuskantar barazanar rage albashinsu da kashi 25 cikin 100 idan suka kasa hayewa gasar cin Kofin Zakarun Turai a karshen kakar wasa ta bana.

Manchester United wadda yanzu take matsayi na 6 a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar rukunin Firimiya ta Ingila, rahotanni sun nuna da wuya  ta iya gama gasar ta bana a cikin kulob 4 na farko ganin yada take da wasanni masu zafi kuma saura wasanni biyar a kammala gasar.

ADVERTISEMENT

A shekaranjiya Laraba ne kulob din ya fafata da na FC Barcelona na Sifen a wasan Kwata-Fainal a gasar Zakarun Turai inda aka ci shi kwallon daya mai ban haushi, kuma ranar Talata mai zuwa ce za a tantance wadda za ta kai semi-fainal a tsakaninsu idan aka buga wasa na biyu.

Wannan dalili ne ya sa mahukunta kulob din suka yanke shawarar zaftare kashi 25  cikin 100 na albashin ’yan kwallon muddin suka kasa kai bantensu.

ADVERTISEMENT

Rahoton da jaridar The Sun ta Ingila ta kalato, ya nuna kamfanonin da ke hulda da kulob din irin su kamfanin kayayyakin wasa na Adidas ne suka gindaya wa kulob din sharadin muddin ya kasa hayewa gasar Zakarun Turai a badi to za su rage huldar da ke tsakaninsu, wanda hakan ya nuna kulob din zai fuskanci karancin kudin shiga.

A wani taron gaggawa da mahukunta kulob din United suka yi, sun shaida wa ’yan wasan halin da ake ciki, kuma muddin ba su yi kokarin hayewa gasar ba, hakan zai sa a rage musu albashi da kashi 25 cikin 100.