✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rataye matar da ta jefo mijinta daga bene a Kano

Wata Babbar Kotun Jihar Kano  ta yanke hukuncin kisa ga matar da ta jefo mijinta daga saman bene ya rasu. A ranar Juma’ar da ta…

Wata Babbar Kotun Jihar Kano  ta yanke hukuncin kisa ga matar da ta jefo mijinta daga saman bene ya rasu.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce kotun, a karkashin Mai shari’a A T Badamasi, ta samu Rashida Sa’idu mai shekara 31 da laifin kashe mijinta Adamu Ali ta hanyar turo shi daga saman bene.

Rashida ta jefo mijin nata ne daga bene a ranar 20 ga Fabrairun bara, a Unguwar Dorayi da ke Kano, biyo bayan rikici ya shiga tsakaninsu.

Rikicin ya barke ne bayan da ta ji yana waya da wata mace da take zargi budurwarsa ce.

Bayan ta turo shi daga benen ne ya karye a wuya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Rahotanni sun ce Rashida na da ’ya’ya biyu da mai gidan nata, sannan ita ce matarsa ta biyu a lokacin da abin ya faru.

Sun hadu da mijinta ne a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da ke Kano, inda bayan daukar wani lokaci suna soyayya suka yi aure, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Kafin Rashida ta jefo Adamu Ali daga kan benen, sai da ta fara kai wa kishiyarta koke, inda ta sanar da ita wayar da ta ji mijinsu yana yi da budurwarsa, kuma abokiyar zamanta ta ba ta shawarar barinsa ya ci gaba da wayar, amma ta ki, a cewar rahotannin.

Rashida na da damar daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara da ke Kano nan da wata uku idan ba ta gamsu da hukuncin ba.