✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rataye wanda ya kashe ’yar shekara 3 ta hanyar fyade

An yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan  matashin nan da ya kashe yarinya ’yar kasa da shekara uku. Babbar Kotun Jihar Kaduna da…

An yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan  matashin nan da ya kashe yarinya ’yar kasa da shekara uku.

Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya ce ta yanke hukuncin a kan Usman Shehu Bashir bayan ta same shi da laifin yin kisa ta hanyar yi wa yarinyar mai suna Fatima fyade.

A farkon watan jiya ne dai kotun ta dage yanke hukuncin bayan ta bayyana matsayinta game da tuhumar da ake yi wa matashin.

Da yake bayyana hukuncin, Mai Shari’a Kabir Dabo ya ce dukkan bayanai da hujjojin da ake nema a kan an aikata laifin sun tabbata ta hanyar bayanai da kuma rubutun da ya yi da kansa wanda kotu ta gamsu da su.

Haka nan kuma kotun ta ce hukuncin zai zamo darasi ga masu tunanin aikata irin wannan mummunan laifi na cin zarafin yara kanana nan gaba.

Mahaifin Fatima, Malam Zakari Ya’u, ya ce an yi adalci

Shari’ar, wadda aka fara ranar 23 ga watan Maris na 2015 ta kawo karshe ne ranar Laraba 3 ga watan Yunin 2020.

Lauyar gwamnatin jihar Kaduna Jummai Dan Azimi ta bayyana gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, mahaifin Fatima, Malam Zakari Ya’u Dahiru ya bayyana hukuncin a matsayin adalci.

Wanda aka yanke wa hukuncin na da damar daukaka kara daga nan har wata uku masu zuwa.