✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a sake bin hukuncin Zimmerman wanda ya kashe bakar fata Martin a Amurka

Hukumar Shari’a ta Amurka na duba yiwuwar sake bibiyar hukuncin shari’ar George Zimmerman mai gadi farar fata da ya kashe bakar fata Tarbon Martin. Sashen…

Hukumar Shari’a ta Amurka na duba yiwuwar sake bibiyar hukuncin shari’ar George Zimmerman mai gadi farar fata da ya kashe bakar fata Tarbon Martin. Sashen shari’ar ya fara gudanar da sabon bincike kan yadda aka yi wa Martin kisan gilla a bara, inda aka kyale kotun jiha ta yi hukunci  kan shari’ar.
A wata sanarwa da sashen shari’ar ya bayar, an bayyana cewa sashen bibiyar miyagun laifuka da hukumar bincike ta FBI da ofishin Babban Mai shari’a na Amurka da ke kula da gundumar Florida na nazarin hujjojin da aka gabatar a matakin tarayyar kasa, tare da shaidu da hujjoji da kotun jihar ta yi amfani da su wajen yanke hukunci.
Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnati za ta sanya “kwararrun masu gurfanar da mai laifi a gaban kotu su yi nazarin hujjojin da ke nuni da keta haddi, ta yadda za sake gurfanar da mai laifin.”
Shugabannin bakaken fatar Amurka sun yi zanga-zanga kan hukuncin kotu na sallamar George Zimmerman, wanda ya kashe matashin bakar fata, Traybon Martin, inda suka bukaci hukumomi su sake gurfanar da wand aake zargi, a matsayin tuhumar Gwamnatin Tarayya.
Benjamin Jealous, shugaban kungiyar kare muradun mutane masu launi (NAACP), wannan kungiya daukacin bakaken fatar Amurka na cikinta, ya ce laifin da Zimmerman ya aikata, a matsayinsa na farar fata, har ta kai ga ya harbi Martin da bindiga ya kashe shi, ya zama babban ma’auni ga sashyen shari’a.
Duk da cewa alkalan Sanford da ke Florida, sun amince da cewa Zimmerman ya jajirce kan cewa kariyar kansa ta s aya halaka Martin, a ranar 26 ga Fabrairun bara, an ji cewa yana kiran ’yan sanda, inda ya yi amfani da kalmomin kaskanci na “punks” da “ these” wato wadannan ’yan iskan makada masu tatyar da hankali.
“Idan aka yi la’akari da yadda bakaken fat matasa ke kokawa kan yadda ake kai musu farmaki, babu wata hujja da za ta hana a ce ba wariya ce ta sanya ya yi wa matashi Traybon kisan gila ba,” inji Jealosu.