✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a sallami wanda ya shigo da cutar Kurona Najeriya daga asibiti

Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiyodun, ya bayyana cewa mutumin nan dan kasar Italiya da ya shigo da cutar kurona Najeriya ya murmure kuma ana dab…

Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiyodun, ya bayyana cewa mutumin nan dan kasar Italiya da ya shigo da cutar kurona Najeriya ya murmure kuma ana dab da sallamarsa daga asibiti.

Gwamnan ya shaida hakan ne a sa’ilin da manyan jami’an kamfanin simintin Lafarge suka ziyar ce shi a fadar gwamnatin jihar da ke Abeokuta wato kamfanin da dan kasar Italiyar ke yi wa aiki.

Gwamnan, ya ce gwamnatin jihar ba zata yi sako sako da cutar murar mashakon ba, kasancewar jihar Ogun Jihar ce da ke da tarin masana’antu da kwararru da ke zuwa daga kasashe daban daban, ya ce hukumar kiwon lafiya ta duniya tare da hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya na taimakon jihar a yunkurin da take na hana yaduwar cutar.