✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sassauta dokar hana ibada a masallatai da coci-coci

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sassauta dokar hana taro a wuraren ibada daga ranar 1 ga watan Yuni. Kwamiti mai yaki da annobar coronavirua na fadar…

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sassauta dokar hana taro a wuraren ibada daga ranar 1 ga watan Yuni.

Kwamiti mai yaki da annobar coronavirua na fadar shugaban kasa ne ya shaida haka a bayanan da yake fitarwa a ko wace rana,

A cewar kwamitin sassaucin na zuwa ne a karkashin wasu ka’idoji da gwamnatocin jihohi suka aminta da su.

Sanarwar tace dokar hana fitar dare da a baya ake farawa daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe za ta koma karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba.

Sai dai dokar hana zirga-zirga da jiha zuwa wata jihar za ta cigaba da aiki kamar yadda take a baya.