Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Za a sauya dokoki don saukaka rabuwar aure a Ingila

Sakataren Shari’a na Birtaniya David Gauke

Za a yi wa dokokin saki a Ingila da Wales garambawul ta yadda ma’aurata za su iya rabuwa da sauri kuma cikin sauki.

A yadda dokokin suke a yanzu dole ne sai daya daga cikin ma’auratan ya zargi daya da zina ko wata dabi’a mara kyau kafin a  fara maganar rabuwar.

ADVERTISEMENT

Nan gaba idan aka yi wa dokar gyara, ma’aurata za su bayyana cewa suna son rabuwa saboda zamansu ba zai yiwu ba sam-sam.

Haka kuma idan  har daya daga cikin ma’uratan yana son rabuwa, to, dole ne a rabu, ko da dayan ba ya so.

ADVERTISEMENT

Sakataren Shari’a na Birtaniya Dabid Gauke ya ce sauyin zai kawo karshen suka ko dora laifin da ma’urata kan yi wajen gabatar dalilin neman kashe aure.

Wannan ya biyo bayan hukuncin Kotun Kolin kasar na kin amincewa da sakin da wata mata ta nema daga mijinta, bayan da mijin ya ki amincewa su rabu.

Tini Owens mai shekara 68 wadda ta fito daga yankin Worcestershire na son rabuwa da mijinta da suka yi shekara 40 tare saboda ta ce ba ta jin dadin zama da shi.

Amma kuma mijin mai suna Hugh ya ki yarda ya sake ta, kuma a kan haka Kotun Kolin ta yi watsi da bukatar matar ta neman saki, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Wanda hakan ke nufin za su ci gaba da zama a matsayin ma’aurata har zuwa shekara ta 2020.

Babbar Mai shari’a ta Birtaniya, Baroness Hale, wadda tana daya daga cikin masu yin wannan shari’a ta dade tana neman a yi wa dokokin gyara, tana cewa babu adalci a cikinsu.

Sababbin dokokin sun tanadi mafi karancin wa’adi na wata shida na rabuwa daga lokacin da aka shigar da karar neman kashe aure.

A karshen wannan wa’adi, za a bukaci wanda ke son a raba auren ya kara tabbatar da cewa lallai yana kan bakarsa ta neman a raba auren kafin a bayar da damar sakin.

Gwamnati ta ce wannan wa’adi zai bai wa mutum dama ya yi tunani a kan rabuwar, ko zai iya sauya shawara.

Haka kuma bayan wannan  dukan ma’auratan za su iya neman rabuwa gaba dayansu.

An dauki wannan mataki ne na sabunta dokokin bayan tuntubar jama’a da aka yi tsawon mako 12, wadda ta nuna jama’a sun amince da haka sosai.

Mista Gauke ya ce yin garambawul ga dokokin na shekara 50 zai iya hana rikici tsakanin iyaye, wanda yawanci ke bata rayuwar ’ya’yansu.

A bisa tanadin dokokin da ake da su yanzu, idan daya daga ma’aurata ya zargi daya da zina ko  wata dabi’a mara kyau a matsayin dalilin neman saki, to shari’ar za ta iya daukar daga wata uku zuwa shida, kafin a tabbatar da rabuwar.

Amma kuma idan neman sakin ya kasance ba mai wadannan dalilai ba ne, to rabuwar za ta iya daukar dogon lokaci.

A nan sai ma’aurata sun gabatar da shaidar da za ta tabbatar cewa ba sa rayuwa tare, wanda hakan zai hada da cewa suna zaune a gida daya, amma kuma ba sa kwana a gado daya, zuwa wani lokaci.

A Ingila da Wales za a iya fara shirya kashe aure ne bayan shekara biyu idan dukkan ma’auratan biyu sun yarda a rabu, amma kuma shekara biyar idan daya bai yarda da rabuwar ba.

Amma a Scotland wa’adin zaman farawar shekara daya ce idan dukkan ma’auratan sun yarda a kashe auren, idan kuma daya bai yarda ba, shekara biyu ne kamar yadda BBC ya ruwaito.