✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a tallafa wa wadanda harin Sokoto ya rutsa da su

Ma’aikatar Jinkai da Agajin Gaggawa ta kasa ta umarci hukumomin da ke karkashinta su mika kayan tallafi ga wadanda harin ‘yan bindiga ya shafa a…

Ma’aikatar Jinkai da Agajin Gaggawa ta kasa ta umarci hukumomin da ke karkashinta su mika kayan tallafi ga wadanda harin ‘yan bindiga ya shafa a jihar Sakkwato

A wata sanarwa da ta fitar, Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa Sadiya Umar-Farouk ta ce tuni ta umarci hukumomin da su gaggauta shiryawa tare da aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar ta Sakkwato don ganin an mika musu kayan tallafin.

“Ma’aikatarmu za ta kasance tare da al’ummar da abin ya shafa a wannan mawuyacin halin da suke ciki sakamakon wannan iftila’in na mummunan harin ‘yan bindiga ta hanyar ba su tallafin da suke bukata”, in ji ministar.

Hajiya Sadiya ta kuma yi Allah-wadai da harin, tana mai mika sakon jajenta ga gwamnatin jihar da al’ummar Sabon Birni wadanda harin ‘yan bindigar ya daidaita, tana mai addu’ar Allah Ya kiyaye aukuwar hakan a gaba.

Ministar ta ce abin takaici ne yadda ‘yan bindigar ke cin karensu babu babbaka ta hanyar kai munanan hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Kimanin mutane 70 ne dai rahotanni suka tabbatar sun rasa ransu sakamakon wani mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai a makon jiya a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar ta Sakkwato.