✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi takaitaccen biki wajen  rantsar da Shugaba Buhari

Bikin rantsar da Shugaba Buhari a zango na biyu da zai gudana a ranar 29 ga watan Mayu zai kasance, ba tare da wani gagarumin…

Bikin rantsar da Shugaba Buhari a zango na biyu da zai gudana a ranar 29 ga watan Mayu zai kasance, ba tare da wani gagarumin shagali ba, inda aka tura manyan bukukuwan zuwa ranar 12 ga watan yuni.

Domin za a maida wannan rana a karon farko ta zama ranar Dimokuradiyya ta kasar nan.Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed shi ne ya bayyana hakan, yace an cimma wannan matsaya ne a taron majalisar zartarwa da ya g abarai ta duniya da za a yi a ranar 20 ga watan Mayu a birnin Abuja udana a ranar laraba data gabata.

Ministan yace tuni an aiken da takardun gayyata ga shugabannin kasashen duniya da su halarci bikin na 12 ga watan yuni a matsayin ranar Dimokaradiyya, domin shi ne rana ta farko ta 12 ga yuni data fado a shekarar da aka gudanar da zabe. Don haka an dauki matakai na tabbatar da wannan rana ta zama ranar Dimokadiyya,yace bikin rantsarwa da kuma ranar Dimokaradiyya za a rinka yi a ranar 12 ga watan yuni.

Lai Mohammed ya kara da cewar kasar nan, ba zata iya gudanar da manyan bukukuwa 2 ba, a dan takin mako biyu ba, kacal.Yace sauran batutuwan da suka jibanci bakukuwan guda 2 za a bayyana su a ranar bikin manema l