Da Dumi Dumi

Za a yi wa Ali Nuhu gwajin coronavirus

Ali Nuhu
Ali Nuhu

Fitaccen jarumi, furodusa kuma darakta a Kannywood na cikin wadanda aka umarta su killace kansu domin a gwada su kan cutar coronavirus.

Sauran wadanda za a gwada sun hada da furodusa Abubakar Bashir Maishadda, da mawaki Ado Gwanja da darakta Hassan Giggs.

Su dai wadannan jaruman sun halarci taron karrama ’yan fim ne na African Magic Viewers’ Choice Award (AMVCA) karo na bakwai, wanda aka yi ranar 14 ga Maris, a Legas.

Gwamnatin Jihar Legas ce ta sanar da cewa duk wadanda suka halarci bikin, ana zaton sun yi mu’amala da wani wanda aka tabbatar yana dauke da cutar ta Covid-19. Don haka ta bukaci duk wanda ya zo ya je a gwada shi.

Sauran wadanda suka halarci bikin sun hada da 2Face da Sanata Dino Melaye da Mercy Ike da Basketmouth da sauransu.

ADVERTISEMENT

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban wani kamfanin shirya fina-finan Hausa da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, “za a gwada shi a kan Covid-19. Ka san sun je taron nan na Legas.”

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya