Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Za a yi wa masu garkuwa da mutane daurin rai da rai

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan

Za a yi wa masu garkuwa da mutane daurin rai da rai

Majalisar Dattawa ta amince da dokar yanke hukuncin daurin rai da rai ga masu garkuwa da mutane.

Sabuwar dokar ta ranar Talata ta yi kwaskwarima ga sashe na 364 na kundin manyan laifuka, daga daurin shekara goma zuwa daurin rai da rai ga masu garkuwa da mutane.

Amincewa da kudurin dokar wadda Sanata Oluremi Tinubu ta gabatar ya biyo bayan mika rahoto a kansa da Kwamitin Majalisar kan Hakkin Dan Adam wanda Sanata Opeyemi Bamidele yake jagoranta ya yi.

Yayin tsokaci a kan sabuwar dokar, Sanata Opeyemi Bamidele ya ce karuwar matsalar garkuwa da mutane a fadin Najeriya da asarar rayuka da take jawowa, ta isa zama hujja ga Majalisar ta dauki matakin da fatan zai zama gargaji ga masu aikata laifin.

Sabuwar dokar ta kuma cire bambancin jinsi kan masu aikata fyade, tare da tsawaita wa’adin yanke wa masu laifin hukunci zuwa sama da wata biyu.

Idan shugaban kasa ya rattaba hannu a kan dokar, za ta fara aiki a manyan kotunan tarayya da kuma kotunan Kudancin Najeriya da ke amfani da kundin manyan lafuffuka.