✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi zabe a Borno da Yobe da Adamawa – Jega

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce za ta gudanar da zabe a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da suke karkashin dokar ta-baci.Shugaban hukumar,…

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce za ta gudanar da zabe a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da suke karkashin dokar ta-baci.
Shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega ne ya bayyana haka a hirarsa da gidan rediyon BBC Landan a shekaranjiya Laraba, inda ya ce matsalar tsaro babbar kalubale ce ga gudanar da zabe, amma kuma za su yi iyakar kokarinsu don ganin cewa an yi zabe a daukacin kasar nan.
A watannin baya, an bayyana fargabar cewa barazanar tsaro a jihohin uku na Arewa maso Gabas saboda hare-haren ’yan Boko Haram na iya janyo cikas a zabubbukan 2015.
Farfesa Jega ya ce hukumar na kokarin sabunta rijistar zabe don gudanar da sahihin zabe a shekarar 2015.
Shugaban na Hukumar INEC ya kara da cewa sun soma tantance jami’an zabe domin tabbatar da kauce wa magudi da aringizon kuri’u a zaben na 2015.