✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a zuba jarin Naira biliyan 610 don bunkasa masakun Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniya ta hannun Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari da wata Masana’antar kasar China mai suna Shandong Ruyi, inda za…

Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniya ta hannun Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari da wata Masana’antar kasar China mai suna Shandong Ruyi, inda za a zuba jarin Dala biliyan biyu don farfado da masakun kasar nan.

Yarjejeniyar za ta bai wa Najeriya damar kafawa da tsara masakun da za rika samar da suturun sawa masu inganci. Za a kafa masana’antun ne a jihohin  Katsina da Kano da Abiya da Legas. Zuba jarin a cewar Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari, ta hada da sanyawa da kuma inganta masaku da noman auduga don yin amfani da ita a masaku. Bugu da kari, ta kuma hada da sarrafa kimanin tan biliyan dubu 3 na auduga a masakun, inda ake sa ran samar da kimanin kashi 20 cikin 100 na bukatar da ake da ita a Afirka baki daya.

Yarjejeniyar kuma za ta sanya a samu sarrafa auduga da masaku z asu rika yin amfani da ita a cikin gida da kuma fitar da ita zuwa waje. A bisa bayanan da aka samo daga ma’aikatar daga 1980 zuwa 2016, kimanin masaku 145 suka durkushe sakamakon ci baya da tattalin arzikin kasa ya fuskanta. kalubalen matsin tattalin arzikin kasa ya janyo masakun da suke da dimbin ma’aikata sun koma kufai, inda suke iya daukar ma’aikata ’yan kalilan a yau.

Wasu daga cikin kalubalen da masakun suke fuskanta sun hada da fasa-kwaurin shigo da kaya daga ketare da rashin ingantacciyar wutar lantarki da rashin samar da tsayayyiyar doka da rashin samun ingantacciyar auduga mai kyau saboda rashin ingantaccen iri.

Ministan Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari, Hajiya A’isha Abubakar, ta bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya tana sane da muhimmancin da fannin yake da shi musamman wajen samar da ayyukan yi da kuma rage zaman kashe wando a tsakanin ’yan kasa da kuma yakar talauci.

“A bisa kokarin da Gwamnatin Tarayya take yi na daukaka fannin da kuma ciyar da shi gaba, ta sanya fannin a cikin jeri na uku daga cikin shiyoyi shida na musamman da za a kirkiro a cikin wannan shekara. Don haka Gwamnatin Tarayya tana yin iya kokarinta wajen tallafa wa fannin ta hanyar zuba dimbin jari a fannin sutura, inda hakan zai taimaka wajen rage farashin auduga da kayayyakin sanyawa.