Za ka iya noman shinkafa da alkama ko da an samu karancin ruwa da kaso 40 – Nazarin Masana

Masana daga Cibiyar Nazarin Alkama da kuma Shinkafa ta Kasa da Kasa, (CIMMYT) tare da wata cibiya takwarta a nahiyar Asiya mai suna BISA a takaice da hadin gwuiwar Jami’ar Thapar sun nuna yadda manoma za su iya noman shinkafa da alkama da kaso 40 kawai na ruwan da ake bukata ta amfani da sabuwar fasahar noma na yin bayi da kuma shuka amfanin.

Sakamakon binciken nasu ya nuna cewar, manoman za su iya noma kwatankwacin abin da suke nomawa ko kuma fiye da abinda suka saba samu ta hanyar amfani da dabarun zamani, kuma su samu riba.

Ko da yake, an gudanar da binciken ne a yankin arewa maso yammacin Indiya-yankin da ya shahara da noman shinkafa da alkamar, amma za a iya dabbaka shi a kasashe irin su Najeriya inda gurgusowar hamada da kuma sauyin yanayi ke matukar barazana ga manoma da ma samar wa da kasa abinci.

Cibiyar ta CYMMYT, ta bada rahoton cewa masanan sun jarraba dabaru iri-iri da za su tabbatar da ragewa manoma yawan kudi da kuma da kuma ruwan da suke bukata wajen noman wadannan kayayyakin amfanin gonan. Sun kuma ce sabuwar fasahar za ta kuma taimaka gaya wajen sinadarin Nitrogen na takin da za a zuba wa gonar shinkafar ko kuma alkamar da zai bukaci kaso 20 cikin 100 kawai na sinadarin.

Sai dai nazarin masanan ya nuna cewa noman shinkafa da kuma alkama a yankin Kudancin Asiya na zai zama cikin barazana sakamakon abinda suka ce raguwar ruwayen da ke kwance a karkashin kasa suke yi a kullum, sakamakon yadda ake zuko ruwayen domin yin bayi wa gonakin shinkafar da alkamar da kuma yadda sauyin yanayi ke shafar hakan.

ADVERTISEMENT

A cewar masanan, matsaloli irin na yawaita ko kuma ambaliyar ruwayen da ake bayin gonakin da su da ma gajiyar da kasar noman ke yi da kuma kona sinadaran ciyawar amfanin gonaki-wadannan na haifar da babbar barazana ga noman shinkafa da kuma alkamar. Dan haka masanan ke ganin sabuwar dabarar da suka bullo da itan, a zaman ita ce kawai mafita ga makomar noman shinkafa da alkama a nan gaba.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya