✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ba Zamfara karin kudi – Gbajabiamila

Shugaban Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, ya yi alkawarin ganin an sama wa Jihar Zamfara karin tallafi a kasafin kudin bana, don samun kudin kara…

Shugaban Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, ya yi alkawarin ganin an sama wa Jihar Zamfara karin tallafi a kasafin kudin bana, don samun kudin kara gina jihar da samar da ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar al’ummar jihar.

Shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki domin ya tattaunawa da masu ruwa-da- tsaki a jihar kan hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin tsaro da ke kawo tarnaki ga jihar.

A lokacin ziyarar, ya bayar da gudunmawar kayan abinci ga ’yan gudun hijira hare-haren ’yan bindiga ya shafa, kuma ya yi alkwarin cewa Majalisar Dokoki ta Kasa za ta yi bakin kokarinta wajen ganin cewa an tallafa wa jihar musamman ta hanyar kasafin kudi domin gudanar da ayyukan ci gaba da za su farfado da rayuwar jama’a.

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle ya yi alkawarin bai wa majalisar duk hadin kai domin ganin  an samu saukin matsalolin tsaro  da ke addabar jihar.

Gwamna Matawalle ya ce, “Makonni kadan bayan hawanmu karagar mulki, mun fara tattaunawa da ’yan bindiga da kuma ’yan sa-kai, don kawo karshen matsalar da ake fuskanta. Bayan fara tattaunawar, mun yi kokarin kubutar da mutum 113 da aka yi garkuwa da su.’’

Ya ce cikin wadanda aka kubutar, mutum biyu ’yan kasar Nijar ne, 11 kuma daga Jihar Sakkwato sai daya kuma dan Katsina sauran kuma duk ’yan Jihar Zamfara ne.

Jihar Zamfara ta jima tana fama da matsalar tsaro lamarin da ya kai ga hallaka mutane da yawa da kuma yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, inda ya yi kamari ya shafi sauran jihohi makwabta irin su Sakkwato da Katsina.

Gwamnatin tarayyar Najeriyar ta sha bullo da matakan yaki da wannan matsala ta tsaro a jihar ta Zamfara, amma lamarin kusan ana ganin ya gagara duk da matakan tura sojoji da ake yi.