Daily Trust Aminiya - Za mu binne Jam’iyyar PDP a zaben 2015 – Dokta Hakeem
Subscribe

Za mu binne Jam’iyyar PDP a zaben 2015 – Dokta Hakeem

Shugaban rikon kwarya na Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna Dokta Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewa ashirye jam’iyyarsu take ta binne Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2015.
A cewarsa, a yanzu akwai ’yan Jam’iyyar PDP da ke komawa APC da yawa a fadin kasar nan, musamman a Jihar Kaduna.
Dokta Hakeem ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a lokacin da shugabannin jam’iyyar suka zauna domin kafa shuganinin jam’iyyar a jihar.
“A yanzu haka su wane ne ’yan Jam’iyyar PDP? Mafi yawansu tsoro suke su bayyana kansu, musamman a Jihar Kaduna. Saboda haka a yanzu jira kawai muke yi mu binne jam’iyyar a zabe mai zuwa,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa nan ba da dadewa ba PDP za ta rasa mutuncinta domin yawancin ’yan jam’iyyar za su gudu su bar ta.
Dokta Hakeem ya ce babu wata jam’iyyar siyasa a kasar nan a yanzu da ke da tsari mai kyau kamar APC.
Don haka sai ya nemi magoyan bayan APC a Jihar Kaduna su kara hakuri domin nan ba da dadewa ba za a fara yi musu rajista.

texem
More Stories