Hukumar INEC ta ce babu bambancin alawus din da za ta biya masu yi wa kasa hidima da za su yi aikin zabe, inda hukumar ta ce za a biya kowannensu Naira dubu 30,500 ne.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a lokacin da yake bayanin a kan zargin cewa an samu bambanci a alawus din da aka biyan masu yi wa kasa hidimar bayan dage zabe a makon jiya.
A cewar Farfesa Mahmood, duk wanda ya yi aikin zaben yana da Naira dubu 4,500 a matsayin alawus din sanin makamar aiki, sai Naira dubu 1 a matsayin kudin mota da kuma Naira 500 a matsayin kudin abinci na tsawon kwana uku da suka dauka suna sanin makaman aikin.
“Idan kuma aka tura mutum inda zai yi aiki ranar zabe, za a ba su kudin mota da abinci na Naira dubu 9 da 400, wanda ya kama Naira dubu 23 ke nan kowa zai karba. A aikin ranar zaben Shugaban Kasa, za a biya Naira dubu 17,500 ga kowane mai hidimar kasa. Amma tunda ba za a sake koyar da su sanin makaman aiki ba a zaben gwamnoni da majalisun jihohi, sai a biya su Naira dubu 13, wanda idan aka hada jimilla, za a samu Naira dubu 30,500 ke nan,” inji Farfesa Yakubu.