✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu bude Gidauniyar  Bafarawa ne domin samar da zaman lafiya da ci gaban kasa- Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ya taimaka wajen jefa kasar nan cikin wani mugun hali.…

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ya taimaka wajen jefa kasar nan cikin wani mugun hali.

Bafarawa ya ce kamata ya yi a hada karfi da karfe wajen shawo kan lamarin ba wai a riga ganin abin a matsayin abin da gwamnati kadai za ta yi ba.

Bafarawa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a wajen kaddamar da Gidauniyar Attahiru Bafarawa domin samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Bafarawa ya ce saboda yadda kasar ke ciki yanzu, shi ya sa yake shirin hada babban gangami na musamman domin nemo asalin matsalar da kuma samar da yadda za a magance matsalar cikin sauki.

Bafarawa y ace duk da cewa shi dan PDP ne, yana so ne ya shirya taron a Jihar Kaduna, wadda ke karkashin APC Kaduna domin a gane cewa ba siyasa a ciki, kuma kasancewar Kaduna ta fi zama tsakiya a yankin Arewa maso Kudu.

Da aka tambaye shi ko ya zai yi domin a samar da kwanciya da tsanaki tsakanin mutane kasancewar a wannan lamari na satar mutane da kashe-kashe ana zargin juna, sai Bafarawa ya ce, “Wannan ne ya sa muke so mu zauna tare da kowane bangare domin jin tab akin kowane bangare sannan a gano matsalar daga tushe domin a gano yadda za a magance matsalar baki daya.”

Ya kara da cewa asali ya kafa gidauniyar ce saboda taimakon mutane da ci gaban kasa, amma kasancewar ba a ciyar da kasa gaba said a zaman lafiya. Wannan ne ya sa yake neman yadda zai taimaka wajen bas hi nasa gudunmuwar wajen samar da zaman lafiya.