✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu burge masoya Kannywood bayan Covid-19 —Maishadda

Masu ruwa da tsaki a harkar shirya finan Hausa sun ce suna nan suna tanadi don ci gaba da kawo wa masoyansu kayatattaun fina-finai da…

Masu ruwa da tsaki a harkar shirya finan Hausa sun ce suna nan suna tanadi don ci gaba da kawo wa masoyansu kayatattaun fina-finai da zarar an janye dokar kulle.

Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilian Aminiya ta wayar tarho a kan halin da masana’antar ke ciki yanzu, da kuma shirye-shiryen da suke yi ganin cewa an fara sassauta dokar ta kulle a fadin Najeriya.

“Duk da cewa komai ya tsaya cak, in Allah Ya yarda za mu dawo da karfinmu fiye da yadda muke a da.

“Mun shirya fara nuna fina-finanmu a sinima irinsu ‘Fati’, da ‘Bana Bakwai’ da ‘So da So’”, inji shi.

Mai shadda ya kara da cewa sun kuma shirya domin ci gaba da daukar wani fim wanda ya tattara manyan jaruman Kannywood da Nollywood,

“Bayan nan muna shirin karasa fim dinmu ‘The Right Choice’, wanda shi ne fim din Kannywood da ba a taba kashe kudi kamarsa ba.”

Furodusan ya kuma ce, “akwai fina-finan da za mu fara dauka irinsu ‘Tsakaninmu’, da ‘Maryama Kamanni’, da ‘Sauta da Gawa’, da ‘Sarki Goma Zamani Goma’, da ‘Kamal Hassan’,” sannan ya kara da kira ga masoyansu da su ci gaba da kiyaye dokokin hukomomi domin kare kai daga kamuwa da coronavirus.

A game da gudunmuwar da masana’antar ta bayar kan yaki da cutar ta Covid-19, Maishadda ya ce, “mun wayar da kan mutane kwarai da gaske game da cutar da kuma yadda za su kare kansu.”