✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ci gaba da hakar mai a Arewa da sauran yankuna- Kyari

Babban Manajan Darakta na Kamfanin Mai na Kasa, NNPC, Mista Mele Kolo Kyari, ya bayyana cewar kamfanin zai ci gaba da binciken man fetur gadan-gadan…

Babban Manajan Darakta na Kamfanin Mai na Kasa, NNPC, Mista Mele Kolo Kyari, ya bayyana cewar kamfanin zai ci gaba da binciken man fetur gadan-gadan a yankin Arewacin kasar, tare da yankin tafkin Chadi.

Mista Kyari, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da wanda ya gada a kujerar, Dakta Mai Kanti Baru, ya gabatar da shi gaban shugaba Buhari, a fadar gwamnatin Najeriyar yau a Abuja.

An ruwaito shi yana cewa, “Za mu ci gaba da neman hanyoyin hako man a yankunan Arewa da sauran yankunan kan iyakar Najeriyar.”

“Muna da guraren da har yanzu ko a yankin Kudancin kasar ma; wadanda har yanzu ba mu kai ga gano man ba, za mu fadada hakar man ta yadda kowa zai amfana da gajiyar hakan shirin za mu aikata hakan, cikin yardar Allah.”