Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Za mu ci gaba da inganta madarar Hollandia’

Manajan Daraktan Kamfanin Chi Limited da ke yin madarar Yogut na Holandia Mista Deepanjan Roy ya ce zagayen da suka yi a wuraren tande tande da lashe-lashe a sassan Najeriya ya nuna cewa masu amfani da madarar Hollandia suna karuwa sosai sakamakon gamsuwa da dandanon madarar mai dauke da kayan hadi. Mista Roy ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a farkon wannan mako.                                                                                                                                                     Ya ce saboda yadda madarar yogut ta Hollandia take da kayan hadi masu dandanon da jama’a suke so ne ya sa ta kasance wata madogara ga abokan hulda.

Ya ce tun kaddamar da madarar a shekarar 2016 abokan hulda suke bayyana gamsuwarsu da ita, saboda dandano da yanayinta, inda ya cesuna sarrafa madarar Hollandia ce da nau’o’in kayan marmari da suka dace da bukatun ’yan Najeriya.

ADVERTISEMENT

Ya ce za su ci gaba da yin madarar Hollandia a mazubi mai nauyin milimita 315 da nau’o’i masu ban sha’awa da za ci gaba da kayatar da jama’a.

Mista Chijioke Silba, manaja ne a wani kantin sayar da kayan lashe-lashe da shaye-shaye a Jihar Ribas ya bayyana cewa madarar Hollandia ce aka fi saye a kantinsa, inda ya ce bayan gabatar da ita ta samu karbuwa a wajen abokan hulda saboda dandano da mazubi mai jan hankalin masu saye da take da su. “Sanin kowane cewa ’yan Najeriya suna son nau’o’in lemon da aka sarrafa su, a zamanance saboda haka na amince da wannan sabon launin, ina tabbatar maka cewa Hollandia ta yi nisa wajen habaka min ciniki a shagona a nan Ribas,’’ inji Silba, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

ADVERTISEMENT

Sanarawar ta ce wani kwararre a fannin ilimin kwamfuta a Jihar Legas, Mista Dele Yusuf, ya ce da farko an ba shi madarar Hollandia ne lokacin da suke yawon shakatawa shi da abokansa, ya ce na samu gamsuwa tare da nishadi. “Tun daga  lokacin ne na kamu da son madarar Hollandia, saboda haka duk lokacin da za muje cin abincin rana da abokaina sai na sayi madarar domin samun dandano mai dadi da nishad,” inji shi.

Manajan Daraktan Kamfanin Chi Limited, Mista Deepanjan Roy ya ce kamfanin yana aiki tukuru domin gamsar da abokan huldarsu. “Muna farin ciki kan yadda abokan huldarmu suke nuna gamsuwa da kayyayakinmu,” inji shi.

Ya ce za su ci gaba da inganta madarar don gamsar da masu amfani da ita a duk fadin kasar nan.