✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ci gaba da kulle iyakokin kasar nan – Hamid Ali

Shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa, Kanar Hamid Ali (mai ritaya) ya tabbatar da cewar iyakokin kasar nan za su ci gaba da zama a rufe…

Shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa, Kanar Hamid Ali (mai ritaya) ya tabbatar da cewar iyakokin kasar nan za su ci gaba da zama a rufe domin tabbatar da tsaro a Najeriya.

Kanar Hamid Ali ya fadi haka ne a iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da ke Maigatari lokacin da ya kai ziyarar aiki.

Ya ce ba a taba yin aikin tsaro na hada-ka ba tsakanin jami’an Kwastan da ’yan sanda da sojoji da masu tsaron na farin kaya da jami’an shigi da fice don hana ayyukan fasakwauri a sama da shekara 60 sai a wannan karo.

Ya ce ya zama dole su hada karfi da karfe domin yaki da batagari da suke fakewa da sunan shigo da kayan abinci ko kasuwa suna amfani da wadansu jami’an tsaro marasa kishi ana shigowa da kayan da aka hana cikin kasar nan.

Ya nuna damuwarsa game da yadda Jamhuriyyar Nijar take bai wa marasa gaskiya mafaka suke shigowa da motoci da kayan da aka hana ta iyakarta, inda ya ce muddin hakan ya ci gaba da faruwa ba zai yiwu gwamnatin Najeriya ta bude iyakar kasar ba har sai sun zauna da mahukuntan Nijar an tattauna kan matsalolin kasashen biyu.

Shugaban Hukumar Shigi da Fice, Alhaji Muhammed Babandede ya ce iyakar za ta ci gaba da zama a rufe saboda a sama wa kayan da muke nomawa daraja a kasuwanni, kuma hakan zai taimaka wajen bunkasa yanayin tsaro a Najeriya, saboda haka ya hori jami’an tsaron da suka yi hada-ka wajen aiki su hada kai wajen yin aiki tare da tabbatar a tsaro a iyakokin.

Ya kuma shawarci mazauna Jihar Jigawa da wadanda suke gittawa ta iyakar Najeriya zuwa Nijar su tabbatar suna da dukkan takardun izinin fita kafin su fita.

Ya ce idan Najeriya ta bude kofa barkatai kowa zai iya shigowa kasar nan, da mai gaskiya da mara gaskiya, sannan ya shawarci baki su yi rajista domin duk wanda ba ya da rajista za a kore su zuwa watan Janairun badi.