✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu dauki mataki kan kisan mutum 23 – Tambuwal

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya ce gwamnati za ta dauki mataki a kan wadanda suka kai harin da ya yi sanadin mutuwar…

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya ce gwamnati za ta dauki mataki a kan wadanda suka kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane a wani sashe na jihar.

Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya kauyen Gangara da ke karamar hukumar Sabon birni, inda aka kashe mutum 23.

“Muna shirin daukar mataki kan lamarin ban ji dadin abin da ya faru ba,” inji shi.

Da maraicen ranar Laraba ne dai wasu da ake zargin barayin shanu ne suka yi wa kauyen kawanya, suka kashe mutanen, sannan suka sace shanu sama da 1,500, bayan sun kone kasuwar garin gaba daya.

Gwamna Tambuwal ya kuma yi kira ga mutanen yankin su kara hakuri da abin da ya faru kada su dauki doka a hannunsu, su bari hukuma ta yi aikinta.

Wata majiya ta shaidawa Aminiya cewa maharan sun shiga kauyen ne da misalin karfe hudu na maraicen ranar Laraba a kan babura kusan 30; kowanne babur kuma yana dauke da mutum uku ciki har da mata, kuma sanye da kayan soji, lamatrin da ya sa mutanen garin suka dauka sojojon Najeriya ne kafin su fara bude masu wuta.

Maharan sun kuma tafi da tumaki 3,000.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da kai harin har an gano gawar mutum 22 da maharan suka harbe a lokacin da suka shigo garin.

Kakakinta, Muhammad Sadik Abubakar, ya ce a yunkurin da aka yi na kama maharan jami’an tsaro sun yi wa wasu daga cikin wadanda ake zargin rauni, sun kuma kashe daya amma sauran suka tafi da gawarsa.