✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu gina Ruga a Jihar Gombe – Gwamna Inuwa

Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce gwamnatinsa ba za ta fasa aikin gina Ruga da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi ba sannan…

Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce gwamnatinsa ba za ta fasa aikin gina Ruga da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi ba sannan ta dakatar domin amfani Fulani makiyaya a jihar ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne bayan wata ganawa ya yi tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Buhari a Abuja.

Shirin gina Ruga shiri ne da Gwamnatin Tarayya ta yi niyyar kafa wa Fulani makiyaya matsugunai domin daina kara-kainar zuwa kiwo a wurare masu nisa.

Za a samar da ababen saukaka kuncin rayuwa kamar kananan madatsun ruwa da asibitoci da makarantu da mayanka da kasuwanni da asibitocin dabbobi.

Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar dakatar da  shirin ne bayan ya haifar da cece -kuce a tsakanin wasu rukunin jama’a da gwamnatocin jihohin Kudu.

Sai dai kuma Gwamnan Gombe, ya bayyana cewa, “A maganar nan da nake yi da ku yanzu, Gwamnatin Jihar Gombe ta kebe fili mai fadin eka dubu 200, domin aiwatar da shirin Ruga a jihar. Don kawai wasu jihohi sun ki shirin, hakan ba zai sa mu a Jihar Gombe mu ki amincewa da shirin ba. Za su aiwatar da shirin, domin muna ganin cewa zai zama alheri ga Fulani, wadanda a yanzu ke faman wahalalhalun yawon kiwon dabbobinsu. da kuma su kansu manoman”