Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Za mu hada sanatoci da talakawa idan ba su sako musu kudinsu na SURE- P ba – A.Y. Gombe

Za mu hada sanatoci da talakawa idan ba su sako musu kudinsu na SURE- P ba – A.Y. Gombe

Alhaji Adamu Yaro GombeAlhaji Adamu Yaro Gombe da aka fi sani da A.Y. Gombe shi ne shugaban Jam’iyyar PDP na farko a Jihar Gombe, kuma a yanzu shi ne shugaban shirin nan na ba da tallafi don rage radadin karin kudin man fetur da ake kira Sure- P na Jihar Gombe. A tattaunawarsa da Aminiya ya nemi Majalisar Dattawa ta gaggauta sako kudaden Sure-P kimanin Naira biliyan 18 domin amfanin talakawan kasar nan da ta rike saboda biyan bukatun ’yan majalisar ko kuma su hada su da talakawa don daukar matakin da ya dace:

Aminiya: Akwai korafi cewa Majalisar Dattawa ce ta rike kudin tallafin rage radadin karin kudin mai da ake kira SURE – P a matsayinka na shugaban shirin a Jihar Gombe me za ka ce dangane da wannan korafi?
A.Y. Gombe: Ina kira gare su da kakkasusar murya su gaggauta sako wadannan kudade na talakawa na SURE- P, domin mu ba su kudinsu, in kuma ba haka ba za mu sa talakawa su kira su su amsa tuhuma. Domin ba daidai ba ne a sake biliyoyin Naira a bangarorin YouWin da Hukumar FERMA da bangaren aikin titin jirgin kasa da hanyar Ore zuwa Shagamu da hanyar Benin zuwa Anaca da ta Fatakwal, amma kudin da za a ba talakawa don ayyukan kyautata rayuwarsu (Community Serbice) da bai wuce Naira biliyan 18 ba, har yanzu a ki sako su, a ganinmu nema suke yi su kawo wa gwamnati cikas a harkokinta. Sannan ina kira ga Sakataren Labarai na sabuwar Jam’iyyar APC, Alhaji Lai Muhammad ya kama bakinsa ya daina kiran sunayenmu a kafafen watsa labarai yana bata mu shugabannin SURE-P na jihohi, kuma ya daina hada siyasa da addini ko kabilanci domin an kashe biliyoyin Naira a yankinsu na Kudancin Najeriya bai yi magana ba, sai yanzu zai rika surutu a kan kudin talakawa ’yan kadan da ba su wuce Naira biliyan 18 ba. Ina so in gaya masa in bai sani ba, wannan shiri da Shugaban kasa ya bullo da shi ba siyasa ta sa ya bullo da shi ba, don taimakon al’umma ne, kuma shi ne irinsa na farko da ya shafi talakawa kai-tsaye ba a maraya kadai ba har da karkara saboda a lokaci daya an dauki fiye da talakawa dubu uku aiki a fadin kasar nan ana biyansu Naira dubu uku-uku duk wata.
Aminiya:Ka ce za ku sa talakawa su kira ’yan Majalisar Dattawa wane mataki kuke so su talakawan su dauka a kansu?
A.Y. Gombe: Idan ba su saki wannan kudi na talakawa ba, za mu gaya musu cewa su ne suka hana a ci gaba da biyansu kudadensu ba mu ba, domin su suka rike don haka su san yadda za su yi da su.
Aminiya:Kana ganin rashin sake wannan kudin da ’yan majalisar suka ki yi, kamar yadda kuke zargi zai iya kawo wa Shugaban kasar cikas a wurin talakawa ne?
A.Y. Gombe: Wannan ai ba da Shugaban kasa suke yi ba, suna bakin ciki ne da talakawan Najeriya na dan abin da suke samu, amma tunda ba su iya hanawa a bai wa mutum daya a YouWin kudin da ya kai Naira miliyan daya zuwa miliyan 10 kyauta don inganta sana’arsa. Sannan ba ga kudin da ake ba Hukumar FERMA da sauransu ba, me ya sa sai kudin da bai kai komai ba da za a ba talakawa don inganta rayuwarsu da cin gajiyar mulkin dimokuradiyya suke hanawa, kuma bayan talakawan ne suka zabe su? In haka ne sai su hana gaba daya, amma a cikin Naira biliyan 270 sun ba kowa, sun hana talakawa don haka shi ya sa nake kiransu da babbar murya su gaggauta sako wannan kudi domin talakawa su samu sassaucin rayuwa.
Aminiya:Mutane nawa ne ake sa ran za su amfana da wannan Naira biliyan 18 a daukacin kasar nan?
A.Y. Gombe: Kimanin mutum dubu bakwai ne a kowace jiha da ke kasar nan aka shirya za su amfana. Da farko mutum dubu goma-goma ne aka tsara, amma sai aka fara da dubu bakwai-bakwai, saura dubu uku-uku kuma da a ce majalisa ta sake wannan kudi sai a kara daukar wasu mutum dubu biyu wadanda su ma za su amfana.
Aminiya: Kamar a nan Jihar Gombe wadanne irin ayyuka ko sana’o’i ne kuke koya wa mutane?
A.Y. Gombe: A kowace jiha a Najeriya an dauki mutum 24 za a koya musu sana’o’i daban-daban a banagren abin da suka karanta ko kuma abin da gwamnati ta ga shi ya fi dacewa su koya. Mu a nan Jihar Gombe an fara ba mutanen horo a sansanin horar da matasa masu yi wa kasa hidima da ke garin Malam Sidi a karamar Hukumar Kwami tun a ranar 20 ga watan Oktoban bana, kuma za su gama karbar horo a ranar 1 ga watan Nuwamba, sannan zuwa gaba a sake daukar wasu daban a horar da su.