Za mu inganta lafiyar al’umma ta hanyar hana bahaya barkatai-UNICEF

Garin Yammawar Kafawa da Jedawan Fulani garuruwa ne da ke yankin Karamar Hukumar Dambatta a jihar Kano da suka yi fama da cututtuka irin na amai da gudawa da Kwalara da sauran su a baya sakamakon rashin Bandakai da ya sa suke bahaya barkatai a fili.

Ganin ya sa Asusun Kula da Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bullo da wani shiri na WASH wato (Water Sanitation and Hygiene) da suke yaki da tsabtar Masai.

Shirin ya isa wadannan garuruwa biyu a yankin karamar hukumar ta Dambatta, inda al’ummar garuruwan suka yaba da wannan shiri sakamakon da basu san muhimmancin yin bahaya a shadda ba sai a fili sai da UNICEF ta shigo.

Yawan bahaya a fili ba a shadda ba hakan ne yasa asusun kula kananan Yaran na UNICEF yace a Najeriya akwai kimanin mutane Miliyan arba’in da bakwai (47) da basu da matsugunni suke bahaya a fili.

Ganin shirin na WASH da asusun kula da kananan Yaran ya isa garuruwan na Yammawar Kafawa da Jedawa a karamar hukumar Dambatta, wakilin mu ya ziyarci Yammawar Kafawa inda ya tattauna da al’ummar garin.

ADVERTISEMENT

Tawagar UNICEF ta kai ziyarar fadar Hakimin Dambatta, Dokta Mukthar Adnan wanda har ila yau shi ne Sarkin Bai na jihar Kano, da ya godewa tawagar bisa ziyarar da suka kai dan duba yadda shirin wanke hannu da hana bahaya barkatai a fili idan anyi bahaya yake gudana.

Hakimin Dambatta, ya yi Magana ne ta bakin Ado Mukthar Adnan, yace suna godiya ga asusun kula da kananan Yara na UNICEF na yadda aka zabi karamar hukumar Dambatta, wajen hana yin bahaya barkatai.

Yace a karamar hukumar Dambatta gaba daya an rungumi wannan shirin domin da a can baya ana yin bahaya barkatai a fili wanda yasa jama’ar garin suke yawan kamuwa da cututtuka daban daban amma yanzu zuwan shirin an samu sauki jama’a suna tona shadda a gidajen su kuma kamuwa da cutattuka ya yi sauki.

Sarkin ya kuma ce daga zuwan shirin ya umurci Dagatan sa da masu Unguwanni da cewa su bai wa shirin hadin kai dan kare lafiyar su.

Da yake magana a fadar kwararren jami’in watsa labarai na hukumar asusun kula da kananan Yaran ta UNICEF Rabi’u Musa, cewa ya yi zuwan su garin Dambatta da wannan shiri an samu nasara.

Rabi’u Musa, ya kuma ce nasarar da aka samu ne yasa suka zo dan ganin yadda jama’ar suke ci gaba da rugumar shirin dan kare lafiyar su da ta sauran al’umma domin a cewar sa yin kashi a fili ba abun da yake haifar wa sai yaduwar cututtuka.

Binta Abdullahi, Matar aure a garin Yammawar Kafawa, cewa tayi da basu san amfanin wannan shiri na idan suka yi bahaya su wanke hannu ba sai yanzu da aka kawo musu shirin kuma da shaddar su ba ruwan su da marfi sai da aka kawo musu aka gaya musu illar barin ta a bude.

Tace da saboda suna barin shaddan su a bude suna yawan kamuwa da cututtuka na amai da gudawa saboda idan kudaje suka taso daga shadda sai kan abincin su amma tunda suka fara rufewa suka samu sauki.

Binta Abdullahi, ta godewa Allah ta godewa hukumar kula da asusun kula da kananan Yaran na UNICEF na kawo musu wanna shirin game da samar musu da ruwan sha.

Muhammad Sani, daya daga cikin mai bai wa Dattawan garin Shawara yace kafin zuwan WASH basu da shadda Yaran su a bayan gidajen su suke bahaya a fili idan iska ta ta shi sai ta debo kashin zuwa cikin abincin su daga karshe sai cuta iri iri amma zuwan WASH yanzu an samu canji.

Muhammad Sani, ya kara da cewa kafin zuwan WASH ko ruwan sha basu da shi a wata tsohuwar rijiya mai nisan gaba goma sha biyar suke shan ruwa amma yanzu WASH ta tona musu rijiyar burtsatse.

Yace da suna yawan fama da amai da gudawa da kwalara amma yanzu sun samu ruwa tsabtatacce da muhalli mai tsabta.

A cewar Muhammad Sani, garin Yammawar Kafawa, akwai mutane da suka kai yawan dubu daya da dari biyar da saba’in da bakwai, amma ko Firamare da asibiti ba su da shi.

Yace tun da UNICEF ta kawo musu wannan shiri na WASH to suna rokon gwamnatin da ta samar musu da asibiti da Makaranta.

Dan jin ko wane irin kokari hukumomi suke yi akai Shugaban karamar hukumar Dambatta Alhaji Idris Haruna Zago, yace suna kokari kare hakkin al’umma domin duk wani shiri da hukumar kula da asusun Yara na UNICEF ta kawo musu basa wasa da shi.

Idris Haruna Zago, ya godewa UNICEF da gwamnatin jihar Kano na yadda suka yi hadaka wajen kawo shirin kiwon lafiya da tsabtar Masai dan kare lafiyar al’umma.

Yace shi kansa ya san yana kokari abunda yasa ma yake samun nasarori a tsakanin sauran shugabanin kananan hukumomi yan uwan sa saboda ayyukan ci gaba da yake yi.

Ya kuma kara da cewa al’ummar garin Dambatta, da sauran kauyukan dake garin sun karbi shirin sosai musamman ma wadannan kauyuka na Yammawar Kafawa da Jedawa.

Ita dai hukumar UNICEF ta kirkiro yaki da tsabtar Masai ne dan kare yaduwar cututtuka da kuma ganin an shawo kan matsalar yin bahaya barkatai a fili

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya