✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu iya samun nasarar rayuwa daga darussan azumi

A yayin da muka shiga watan ibadar azumi, za mu yi tambihi ne, mu ga yadda za mu iya amfani da darussan azumin, wajen inganta da…

A yayin da muka shiga watan ibadar azumi, za mu yi tambihi ne, mu ga yadda za mu iya amfani da darussan azumin, wajen inganta da bunkasa rayuwarmu ta yau da kullum, yadda za mu iya cin ma nasarar rayuwa da su.

Daya daga cikin darussan da azumi ke koyarwa shi ne hakuri, domin kamar yadda al’amarin yake, mutum zai yi hakurin jure wa yunwa tun daga asubahi har zuwa faduwar rana, na tsawon kwanaki 29 ko 30. Idan har mutum zai iya yin hakurin yunwa da kishirwa haka, ke nan zai iya hakuri da duk wata wahala ko damuwa da za ta same shi. Wannan yana nuna mana cewa, a al’amuran da muke fuskanta na rayuwa, muna da bukatar hakuri. Za mu kasance cikin hakuri wajen zama da abokan zamanmu, kamar makwabta, abokan aiki, iyali da sauransu, domin kuwa abu ne na hakika, za mu rika fuskantar al’amura marasa dadi, ko na bacin rai a zamantakewa da juna. Idan muka sanya hakuri cikin kowane al’amari, sai a zauna lafiya da juna har wannan sabani ko al’amari mara dadi ya wuce. Mafi yawan lokaci, rashin hakuri da yanayi marar dadi, shi ke haifar da rashin jituwa, ya haifar da matsala tsakanin al’umma, wani lokacin ma har ya kawo fada da tashin hankali. Don haka, mu koyi hakuri daga ibadar azumi, sai mu kasance masu nasara a rayuwa.

Juriya ma wata halayya ce mai matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam. Idan mutum ya kasance mai juriya, babu shakka zai kasance mai samun nasarar duk wani abu da ya fuskanta a rayuwa. Cikin darussan da azumi ke koya mana kuwa, har da juriya, domin kuwa irin yadda mutum zai jure yunwa da kishirwa, ya jure da aikata ayyukan alheri da ibada, yana yi mana ishara ne da yadda ya kamata mu zauna a rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar yadda al’amarin zamantakewar mutane yake, ya zama wajibi ga mutum ya fita neman abinci, ya Allah wajen aiki ne ko sana’a da dai sauransu. Aiki kuwa ba dadi gare shi ba, domin ya hada da motsa jiki da wahalhalu iri-iri. Wannan ke bukatar juriya daga mutum. Idan mutum ya jure da wahalar neman abinci, ya jure wa duk wani kalubale da zai ci karo da shi; babu shakka nasara ta zama a hannunsa.

Azumi yana koya wa mutane tsoron Allah. Idan mutum ya kasance mai tsoron Allah, shi ke nan, ba shi da wata matsala a rayuwa. Wannan tsoron Allah da ke tare da shi, zai ba shi damar yin taka-tsan-tsan a cikin dukkan al’amuransa. Ba zai aikata wani abu ba sai ya nazarci abin da zai haifar. Wannan zai sanya ya rika aikata abubuwan da kawai za su kasance na alheri gare shi da sauran al’umma gaba daya. Ba zai aikata duk wani abu ba na sharri ko wanda zai cutar da al’umma. Idan mutum na da tsoron Allah, ba zai aikata rashin gaskiya ba, ba zai ci amana ba, ba zai yi shaidar zur ba, ba zai cuci dan uwansa ba. Ke nan zai zama mikakke kuma wankakke, kamar yadda zai kasance tsarkakakke, mai tsarkin hali da na zuciya. Idan mutum ya kasance haka kuwa, shi ke nan ya samu nasarar rayuwa. Shi ne zai zama abin da ake kira, baka lafiya, ciki lafiya. Idan aka samu al’umma suka siffatu da tsoron Allah, babu sauran matsalar rayuwa. Don haka, mu yi amfani da darasin azumi, mu kasance masu tsoron Allah a rayuwarmu gaba daya.

A rayuwar mutum, madamar yana son cin ma nasara, ya zama wajibi ya tunkari aikata abin da ya dace. Babu wani abu kuwa da ke koya irin wannan darasin kamar azumi. Azumi ne ke bukatar mutum ya kasance mai hankali, mai hikima, mai tunani, mai tausayi da jinkai da kaunar al’umma da ci gabansu. Abin tambaya a nan shi ne, a lokacin da mutum ya kasance mai wadannan halaye da muka zana a sama, me ya rage masa daga samun nasara? Ka fadi kuma ka kara fadi da babbar murya, madamar mutum ya kasance mai tausayi da jinkan al’umma, zai kaance abin kauna ga al’umma. Idan al’umma suka kasance cikin kaunar juna kuwa, to za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa. Idan wannan ta samu kuwa, shi ke nan nasara ta tabbata.

Babu shakka, akwai kyawawan al’amura, abin koyo daga azumi. Ba za su kidayu ba a wannan takaitaccen fili. Abin da kawai ya kamata mu yi shi ne, mu lalubo su, mu nazarce su, mu sanya su cikin jerin abubuwan da za mu rika aikatawa; wanda haka zai zame mana fitila kuma ya zama jagora zuwa ga samun nasarar rayuwa. Irin wadannan abubuwa kuwa, kamar yadda muka dan bayyana su a sama, sun hada da hakuri, juriya, aiki tukuru, yin gaskiya da adalci tsakanin al’umma da sauran irinsu. Haka kuma, ya zama wajibi mu kaurace wa duk wani abin ki da azumi ke ki, madamar dai muna son cin ma nasara. Wadannan abubuwa kuwa sun hada da karya, cin amana, zamba, sata, almubazzaranci da sauran muggan dabi’u.

Muna rokon Allah Ya yi mana jagora cikin al’amuran rayuwarmu, Ya ba mu dacewa da aikata ayyukan kwarai a kowane lokaci. Allah Ya sanya mu dace, mu kasance cikin masu rabo, mu kasance ’yantattu a wannan wata mai albarka, amin.