✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kafa masana’antar sarrafa dabino da aya a Jihar Katsina – Kungiya

Kungiyar Masu Sayar da Dabino da Aya ta Jihar Katsina ta ce, za ta samar da masana’antar da sarrafa dabino da aya a jihar domin…

Kungiyar Masu Sayar da Dabino da Aya ta Jihar Katsina ta ce, za ta samar da masana’antar da sarrafa dabino da aya a jihar domin tafiya daidai da zamani da kuma sama wa jama’a musamman matasa ayyukan yi. Shugaban Kungiyar Malam Sama’ila Ibrahim ya bayyana haka a hirar da ya yi da wakilin Aminiya a Katsina.

“Irin yadda mutanenmu ke shiga sako-sako don nemo dabino da aya a cikin jihar ya ba mu damar sanin yadda za mu rika sarrafa su tamkar yadda ake yi musamman a kasashen Labarawa. Saboda mun lura da cewar rashin kula da kuma kokarin yin bincike a kan kowace irin sana’a na mayar da sana’ar baya. Bisa haka ne ya sa muka fara jarraba sarrafa dabino wanda wani a cikin kwali kuma in ba an gaya maka ba sai ka ce daga Saudiyya aka kawo shi. Kazalika, kafa wannan masana’anta za ta ba mu damar sarrafa ayar ta zamo ko dai nikakkiya ko ta ruwa,” inji shi.

Shugaban ya ce, sai dai aiwatar da hakan ba zai yiwu ba sai sun samu filayen da za su gina wadannan masana’antu a shiyyoyin Daura da Funtuwa da Katsina. Shugaban ya ce yayin da suke yi wa Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari fatan alheri tare da taya shi murnar sake zabensa karo na biyu suna nanata kiransu gare shi kan ya juyo kan wannan batu nasu wanda suka ce tuni suka mika kokon bararsu gare shi kuma suna da yakinin zai tallafa wa kungiyar ta fuskoki da dama.

“In har muka samu wannan gudunmawa to za mu zamo ko in ce Jihar Katsina za ta zamo ta farko ta wannan fuska da ta bar wa jama’a abin dogaro da kansu. Kowa dai ya san jihar tana da duk wata hanyar da za a samo wadannan kaya don kaiwa sassan kasar nan,” inji shi.

Shugaban ya ja hankalin ’ya’yan kungiyar da sauran masu sana’o’i a fadin jihar su ci gaba da yin tunani da bincike ta yadda za su zamanantar da sana’o’insu.