✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kawar da shinkafar waje daga kasuwannin Jihar Katsina – MM Beto

Sabon kamfanin casa da gyara shinkafa da ke Malumfashi a Jihar Katsina ya fara aiki bisa kudirin ganin sun kawar da shinkafar waje daga kasuwannin…

Sabon kamfanin casa da gyara shinkafa da ke Malumfashi a Jihar Katsina ya fara aiki bisa kudirin ganin sun kawar da shinkafar waje daga kasuwannin jihar da kuma kasa baki daya. Tun a farkon shekarar 2017 aka samar da wajen casar shinkafar na zamani a garin Funtuwa, amma saboda karancin wutar lantarki da karancin sansamin shinkafar ya sa haka ba ta cinma ruwa ba.

Alhaji Mustafa Ma’azu Mai’auduga shi ne Manajan Daraktan Kamfanin MM Beto, ya ce, yawaitar noman shinkafar da manoman jihar suka yi, ya sa suke da tabbacin samar da ita a jihar. “Ba kamar bara ba, manoma a bana sun rungumi noman shinkafa wanda hakan ya sa za mu iya casa tare da gyara wadatacciyar shinkafa a bana. Koda za a ce za mu samu karancinta to wannan shiri na noman rani a Jibiya, Ajiwa, Malumfashi da Kafur zai taimaka a magance matsalar karancin,” inji Mai Auduga.

Ya kara da cewa, sun fara aikin gyara shinkafar tun daga watan Satumba, saboda haka ya ja hankalin dillalan shinkafa da suka fito daga Legas, Fatakwal, Kaduna, Kano da Abuja. cewa, “Injinanmu na da karfin da za su casa tan 2 a cikin awa guda, sannan muna yin aiki sau biyu a kullum, wato safe da dare. A yanzu dai mun fitar da buhu 300. Kasancewar injin namu yana sabo sai muka fara gwaji daga buhu 40 da 60 da 160 har ta kai a yanzu mun yi 300. Nan gaba kadan zai ci gaba da aiki sosai.”

Ya ce, saboda suna aiki da janareto ya sa kowane buhu yake kama musu a kan Naira dubu 13 da 800 kan farashin kamfani.

Manajan ya fadi a lokacin da suke zagaya masana’antar da wakilinmu cewa babu wata masana’antar casar shinkafa da ta kai MM Beto girma a duk yankin Funtuwa. “Har yanzu ba mu ci gaba da aikin ba kamar yadda ya kamata saboda ba mu hada kayan tafasawa da busar da shinkafar ba. Muna dai casar ce a yanzu a wajen masana’antar, hakan ne ma ya sa muke yin buhu 300 a kullum. Ka san shi sabon inji yana fara aiki ne a hankali kafin ya warware a ci gaba da aiki da shi sosai,” inji shi.

Kazalika, ya kara da cewa, suna amfani da mai durom 2 a kullum, kuma kudin litar man tana kamawa Naira 212, hakan ya samo asali ne daga karancin wutar lantarki da ake fama da ita a garin Malumfashi da kewaye.

Kamar yadda wani ma’aikacin kamfanin mai suna Abdul’aziz Abdulrahman ya ce, wannan shiri na noman shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta kawo, ya haifar da samar da wannan masana’anta ta casa ta MM Beto, haka kuma shirin zai kawo raguwar talauci tare da rage zaman kashe wando wanda kan jawo shiga aikata laifuffuka a tsakanin al’umma.

Muhammadu Auwal wani dilalli ne daga Jihar Kano, ya ziyarci wannan masana’anta domin gani da ido kan yadda yake gudanar da ayyukansa, ya ce ya gamsu da yadda ya ga suke samar da kyakkyawar shinkafa da kuma yadda suke adana ta a cikin buhu. Ya shaida wa Aminiya irin gamsuwarsa, nan take ma ya bayar da odar buhu 600 domin kai wa abokan harkarsa a gidan Singer da ke Kano a matsayin samfuri.