✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za mu magance matsalar ruwan sha a Bauchi’

Hukumar Ruwa ta Jihar Bauchi ta bayyana qoqarin da take yi na samar da ruwa lita miliyan 75 ga daukacin al’ummar jihar a qoqarin da…

Hukumar Ruwa ta Jihar Bauchi ta bayyana qoqarin da take yi na samar da ruwa lita miliyan 75 ga daukacin al’ummar jihar a qoqarin da take yi na magance matsalar qarancin ruwan sha a birnin Bauchi da kewaye.

Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Aminu Aliyu Gital ne ya sanar da haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai dangane da irin qoqarin da suke yi na gudanar da ayyukan samar da ruwa a jihar.

Ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi da hadin gwiwar Bankin Duniya suna qoqarin yin babban aiki domin samar da ruwan sha amma kafin a kammala aikin tuni sun dauki matakai kan yadda za a samar da ruwan sha ga al’umma cikin sauqi ba tare da samun matsala ba.

Injiniya Gital ya ce a yanzu haka sun dauki matakan gyara manyan hanyoyin tura ruwa da suka shafi fiye da shekara 50, “Wadannan hanyoyin ruwa na garin Bauchi na san sun girme ni kuma na san na bai wa shekara 50 baya, kuma duk bututun da ya yi shekara 50, ya kamata a ce ya kai matsayin da za a canja shi, saboda haka za a canja tsofaffin bututu da a halin yanzu ma suna yawan zubar da ruwa. Kuma akwai unguwannin da suka qaru a garin Bauchi wadanda yanzu ba su da bututun ruwa, su ma za a yi amfani da wadannan bututu a ja musu ruwa, kuma akwai manyan bututu da suka dauko ruwa daga Madatsar Ruwa ta Gubi zuwa manyan tankunanmu na Warinje da Buzaye su ma sun tsufa. Ka ga in ana maganar bututun qarfe ya yi kusan shekara 30 su ma za a canja su da wadannan manya saboda a samu qarin shigowa da ruwa. Wadannan su ne tallafin da Bankin Duniya suke yi wa gwamnatin jihar,” inji shi.

“Idan ka ziyarci Madatsar Ruwa ta Gubi kanta ruwan da matatar ana gyara su kuma ana fadada madatsar saboda a samu tabbacin cewa tana da qwari da qarfi, kuma ta ci gaba da samar da ruwa yadda take samarwa a yanzu da fadada ta yadda za a ci gaba da samun lita miliyan 75 kowace rana, wannan shi ne zai biya buqatar ruwa a garin Bauchi da kewaye har zuwa shekarar  2025,” inji shi.

Manajan Daraktan ya yi watsi da fargabar da ake yi cewa madatsar ruwa ta Gubi za ta fashe ta yi ambaliya, “Babu wannan fargabar a yanzu, na san shekara  4 zuwa 5 baya akwai lokacin da kana cikin qauyen za ka ji ruwan madatsar ruwan yana qugi, wannan kuma abu ne wanda dama an san haka zai iya faruwa, amma a qarqashin wannan tallafi na Bankin Duniya akwai matakan da aka dauka don ganin an qara qarfafa madatsar ruwan ta yadda ba za a fuskanci wata barazana ba,” inji shi.

Sai ya roqi jama’a su riqa biyan kudin ruwa kuma su gane cewa ruwan da ake samarwa ga al’umma nasu ne don haka su kula da shi qwarai domin samun ci gaba.