✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu maida martani ga duk tashin hankalin da APC ta nemi yi – Wada

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Kyaftin Idris Wada, ya ce jam’iyyarsu ta PDP za ta maida martani ga duk yunkurin tashin hankali da Jam’iyyar APC ko…

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Kyaftin Idris Wada, ya ce jam’iyyarsu ta PDP za ta maida martani ga duk yunkurin tashin hankali da Jam’iyyar APC ko wani mutum zai yi a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba bana, don kwace wa jam’iyyarsu nasararta a jihar.

Alhaji Idris Wada ya bayyana haka a Sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja, bayan ya sayi takardar nuna sha’awa don tsayawa takarar a zaben da ke tafe, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin Jam’iyyar PDP za su shirya mutane da za su fito domin da tsara dabarun mayar da martani ga duk wani tashin hankali da zai fito daga bangaren jam’iyya mai mulki.  Ya ce zaben Gwamna na shekarar 2016 da ya shige wanda ya raba shi da kujerar mulki, an tafka magudi ne don biyan bukatar wannan gwamnati. “Eh, sun yi amfani da tashin hankali a zaben 2016, a wannan lokaci duk wanda ya yi kokarin yin haka, za mu mayar da martani daidai da abin da suka yi mana ko fiye da abin da suka yi.

Ba za mu zuba ido mutane su sace mana zabe ba a wannan karo, za mu tsaya a fafata kan haka. Kuma za mu hada kan ’ya’yan   jam’iyyarmu,” inji shi.                                                                                                                                             Ya ce “Bari in gaya muku a shekarar 2016 ba mu fadi a zaben ba, an sace mana ne, dukka kun san abin da ya faru. A fili yake an sace mana zaben ne. Amma a matsayinmu na wadanda suke da imani da Ubangiji sai muka karbi sakamakon aka wuce wajen. Wannan wata dama ce ga mutanenmu su auna shin suna jin dadi a yanzu fiye da lokacin da nake Gwamna? Su amsa wannan tambaya da kansu?”

Ya ce an jefa al’ummar Jihar Kogi cikin kuncin rayuwa  babu tsaro kowa na barci da ido daya ne. Ya ce hakika Gwamnatin APC ta gaza cika alkawuran zaben da ta daukar wa al’umma, amma al’amura za su koma yadda suke muddim an sake zabarsa domin Jam’iyyar PDP ce kadai mafita ga al’ummar Jihar Kogi.