✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu rage cinkoso a Legas mu tsabtace ta – Ahmad Kabir

Alhaji Ahmad Kabir Abdullahi sabon mai bai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shawara a kan tsare-tsaren birnin Legas ya ce gwamnatin Legas za ta rage yawan…

Alhaji Ahmad Kabir Abdullahi sabon mai bai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shawara a kan tsare-tsaren birnin Legas ya ce gwamnatin Legas za ta rage yawan cinkoso da ake fama da shi a birnin  ta hanyar fito da sababbin tsare-tsare na zamani tare da tsabtace birnin.

Alhaji Ahmad Kabir ya shaida wa Aminiya haka ne lokacin da al’ummar Arewa mazauna Legas suka ziyarce shi a gidansa da ke Agege domin taya shi murna sabon mukamin da Gwamnan ya ba shi na Mai ba shi Shawarar na Musamman a Kan Harkokin Tsara Birane, a matsayisa na dan Arewa mazaunin Jihar Legas kuma jagora al’ummar Arewa na jihar a Jam’iyyar APC.

Shugabannin al’ummar Arewa Mazauna Legas da suka hada da Sarkin Hausawa Alhaji Sani Kabiru da Sarkin Shuwa Arab Alhaji Jibrin Yaya da Shugaban Kungiyar Kare Muradun Arewa bangaren matasa Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu sun ziyarci zauren da aka rantsar da sababbin kwamishinoni da masu bai wa Gwamnan Shawara inda suka rufa wa Ahmad Kabir baya lokacin da aka rantsar da shi.

Sarki Sani Kabiru ya bayyana farin cikinsa tare da na al’ummar Arewa gaba daya bisa mukamin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bai wa dansu, ya ce suna fatan zai yi amfani da gogewa da kwarewarsa wajen ciyar da jihar da al’ummarta gaba, kuma ya yi kira gare shi ya yi kokarin dinke barakar da ke tsakanin ’yan Arewa mazauna Jihar Legas da yin aiki tare da kowane bangare domin cimma nasara. Haka zalika Sarki Sani Kabiru ya yi kira ga al’ummar Arewa mazauna jihar su bai wa Alhaji Ahmad Kabir goyon baya domin ya cimma nasara domin nasararsa nasara ce ga ’yan Arewa mazauna Jihar Legas

A ranar Litinin da ta gabata ce Majalisar Dokokin Jihar Legas karkashin jagorancin Shugabanta Honurabul Madashiru Obasa ta tantance mutum 35 daga cikin 38 da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar mata don nada su a kwamishinoni da masu ba shi shawara, inda ta yi watsi da uku bisa dalilan da ba ta bayyana ba. Sai dai wata majiyar Aminiya ta ce rashin tantance mutum uku na da alaka da rashin cika ka’idojin takardunsu da rashin zuwa hidimar kasa da wasunsu ba su yi ba, haka akwai wanda majalisar ta ladabtar bisa dalilin rashin da’a kafin daga bisani a tantance shi.

Kwana guda da majalisar ta tantance mutum 35, Gwamna Sanwo-Olu ya rantsar da su tare da ba su takardun shaidar kama aiki inda ya nada kwamishinoni 21 da masu ba shi shawara14, wadnda ya yi kira gare su da su jajurce domin ciyar da jihar da al’ummarta gaba.