✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu samar da sabon Irin Gero da zai dace da kowane yanayi – Farfesa Magashi

Ganin yadda Gwamnatoci a kasar nan suke ta kokarin mayar da hankali kan fannin noma domin rage dogaro da man fetur da kuma bunkasa samar…

Ganin yadda Gwamnatoci a kasar nan suke ta kokarin mayar da hankali kan fannin noma domin rage dogaro da man fetur da kuma bunkasa samar da abinci, ya sa gwamnatocin ke kiran ’yan kasa da su koma gona domin bunkasa samar da abinci a cikin gida.

Sai dai rashin bincike daga bangaren malaman manyan Makarantu yana daya daga cikin abun da yake kawo nakasu ga fannin samar da abinci a kasa  da kuma rashin isasssun kudade da za su tallafawa binciken daga bangaren Gwamanti. Wannan yasa Aminiya ta gana da daya daga cikin masana ilimin kimiyyar tsirrai ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha dake Garin Wudil Jihar Kano, Farfesa Auwal Ibrahim Magashi, dangane da sabuwar fasaha da suke kokarin fitowa da ita, ta samar da Irin gero wanda zai dace da kowane irin yanayi. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance da wakilin Aminiya.

Abin da ya ja hankalinmu wajen samar da sabon irin gero

Sanin kowa ne cewa amfanin malaman manyan makarantu shine su koyar da dalibai sannan su gudanar da bincike da zai taimakawa ilimin kansa da kuma samarwa masana’antu sahihin bincike domin dorewar masana’antun da kuma samar wa gwamnatoci hanyoyin da za subi wajen samar wa ‘yan kasa abubuwan more rayuwa da sauran su.

Babban dalilin da yaja hankalina wajen fara wannan binciken shine gwamnatin Kasar Sin tana shirya wani taro wanda ya shafi bincike a kan noma duk shekara. Tana gayyatar masana daga sassan duniya daban-daban domin tattaunawa yadda za’a inganta noma ko kuma a samar da wata mafita akan iri kaza ko wata matsala da take damun wadansu tsirrai.

Daga nan Najeriya mu uku, aka gayyata domin wakiltar Najeriya wajen wannan taro  kuma a nan na samo wannan iri na gero mai suna ‘’Mai Jelar Dila’’ wato (Fod tail) a turance. Domin ya banbanta da nau’in geron da muka sani na al’ada. Kuma ana sarrafa shi wajen yin abubuwa da dama wanda ya shafi abinci da kuma sarrafa shi domin masana’antu.

Wannan dalilin shiya ja hankalina wajen dauko irin domin yin nazari a kansa da kuma yiyuwar fitowa da shi ga manoma domin fara cin gajiyarsa.

Wannan gero zai dace da kowane irin yanayi

Sakamakon binciken da muka yi, ya nuna mana wannan nau’in na gero mai ‘Jezar Dila’ zai dace da kowane yanayi wanda ya hada da yanayin; zafi da sanyi da kuma lokacin damina. Domin yanzu haka mun yi gwaji na lokacin sanyi da zafi wanda shine muka shuka shi a cikin watan Nuwamba muka girbe shi a Watan Janairu.

Wannan ta sa muka yi tunanin mu samar dashi ga masu noman Rani domin bunkasa noman gero domin cin gajiyarsa, da zarar mun kammala bincikenmu za mu gabatar da shi ga hukumomi domin yin nazari a kansa sannan mu gabatar da shi ga manoma.

Wannan sabon Irin akwai yiyuwar za’a iya noma shi a Kudu

Saboda yawan ruwan sama da yake sauka a kudancin kasar nan yasa basa iya noma gero na mu na al’ada. Amma akwai yiyuwar wannan sabon irin na gero na iya nomuwa a Kudancin Kasar nan saboda gwajin da muke yi ya nuna watakila za a iya nomashi. Sai dai shi Gero baya son ruwa sosai kuma ya fi son zafin rana. To amma nan gaba za mu samar da cikkaken bayani akan hakan idan bincikenmu ya kammala.

Dole sai an yi nazari akan wani lokaci ne zai fi dacewa da noma wannan sabon irin gero a Kudancin kasar nan. Amma dai kawo yanzu mu na ganin akwai yiyuwar noma gero a Kudancin kasar nan.

Noman gero zai taimaka wa tattalin arziki

Bisa ga yadda yanzu duniya ta maida hankali kan sarrafa gero domin abinci da kuma magunguna ya sa manyan masana’antu suna bukatar gero domin sarrafashi don samun riba, musamman wannan sabon geron domin ana sarrafashi wajen samar da madara, da samun sinadarin kiwon lafiya, a na yin burodi dashi da biskit da abincin dabbobi da sauran amfani iri daban-daban. A iya noman gero kadai, gwamnati na iya samar da makudan kudaden shiga domin habaka tattalin arziki kuma ta samar da aikin yi ga ’yan kasa da walwala da kuma kiwon lafiya, domin akwai sama da hanyoyi 18 da ake sarrafa gero da su.

Abin da ya sa ba mu shigo da gwamnati ciki ba

Dalilin da ya sa ba mu shigo da gwamnati cikin wannan shiri ba tunda fari shine ita gwamnati za ta iya shigowa ne kadai idan bincike ya kammala ko kuma ana da bukatar wani tallafi daga wajenta ko kuma kayan aiki ko tana da wani shiri akan wannan binciken namu. Amma kofa a bude take da zarar mun kammala wannan binciken namu na farko to za mu kira taron masu ruwa da tsaki akan fannin noma domin yi musu cikakken bayani akan wannan sabuwar fasaha ta noman gero wato sabon irin gero mai suna (Fod Tail Millet). Akwai ragowar bincike da muke saran gwmnati ta dauki nauyinsa, kamar taron kasa da kasa akan wannan fasaha ta irin gero wanda asalinsa daga kasar Sin wato China mu ka samo shi, domin gwada shi ko zai dace da irin yanayin da mu ke da shi a Najeriya. Kamar sauran abubuwan da ake nomawa irin su shinkafa da dawa da alkama da ridi da sauransu. Za ka gan su nau’i daban-daban, shima gero so mu ke ace akwai nau’insa daban-daban, kamar yadda shinkafa take da nau’i daban-daban.

A taikaice da zarar mun kammala gwajinmu, to zamu gabatarwa gwamnati wannan sabon iri domin ta shigo ciki domin a fadada bincike don cigaban kasa baki daya.

Kirana ga malaman manyan makarantu

Kirana ga malaman Jami’o’i shi ne mu tashi tsaye domin yin bincike da zai taimakawa al’ummarmu. Domin nauyi ne da yake kanmu ba wai kawai muje dakin taro mugabatar da mukala shike nan iya abinda za mu iya yi. Gaskiya wannan kalubale ne mai girma domin duniya ta yi nisa ta bar mu a baya. Ta hanyar bincike ne kadai zamu bada gagarumar gudummawa ga kasar nan. Yana daga cikin dalilin da ya sa gwamnatoci ba sa mutunta malaman jami’a ta hanyar ba su tallafi domin yin bincike shine su malaman ba sa abinda ya dace wajen yin bincike.  Da manyan farfesa-farfesa da ragowar masana za su dage da bincike da sun fitar da kasar nan daga kangin da take ciki, don haka dole mu tashi mu yi tunani sannan mu sarrafa tunanin namu ta hanyar yin bincike. Kuma mu sa kishin kasa da al’ummarmu a cikin rayuwarmu.

Duk wata kasa da ka ga ta cigaba to ma su iliminta sun bada gudunmawa babba, kuma idan ma kudi kake so to ta wannan binciken ma kadai ya isa ka samu kudade masu yawa.

Kirana ga gwamnati da attajirai

Ina kira ga gwamnati da masu hanu da shuni da su taimaka da isassasun kudade domin taimawaka wa masu bincike na gida, domin a inganta albarkatun da Allah Ya hore mana, ba sai mun jira wadansu daga waje sun zo kasarmu sun gudanar da bincike akan albarkatunmu ba domin mu ‘yan kasa, mu muka fi cancanta da yin nazari akan al’adunmu, arzikin kasarmu da zamantakewarmu kuma mu yi nazari ta kowace hanya ce zamu ingantata.

Dole gwamnati ta samar da yanayi mai kyau na karfafar ’yan kasa domin  kaiwa ga gaci. Su kuwa masu kudi wadanda suke da masana’antu su ma su dinga bayar da Kwangilar yin nazari da bincike ga masana na cikin gida, domin su ma su taimakawa bangaren.

Sa’annan gwamnati ta yi wata doka da za ta dinga hukunta duk wani malamin jami’a da aka samu da yin binkcike na bogi, a sa horo mai tsanani domin samar da ingantattun masu bincike nagari.