✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu samar wa Buhari kuri’a miliyan 40 – Shugaban Kungiya

Shugaban Kungiyar Buhari/Osinbajo Dynamic Support Group, Alhaji Ibrahim Usman ya ce a shirye suke wajen samar wa Shugaban Kasa Muhammadu  Buhari kuri’a miliyan 40 a…

Shugaban Kungiyar Buhari/Osinbajo Dynamic Support Group, Alhaji Ibrahim Usman ya ce a shirye suke wajen samar wa Shugaban Kasa Muhammadu  Buhari kuri’a miliyan 40 a babban zaben watan Febrairun 2019 da ke tafe.

Alhaji Ibrahim Usman ya bayyana haka ne a hira ta musamman da Aminiya, inda ya bayyana cewa sun tanadi hanyoyi daban-daban na tabbatar da nasarar Buhari a karo na biyu, don ci gaba da kyawawan ayyukan gina Najeriya.

Shugaban ya kara da cewa a zabubbukan baya Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Kasa ta yi wa mutum miliyan 50 ko 60 rajistar jefa kuri’a, amma a wannan karon an samu kusan miliyan 80 ne, saboda yadda mutane suka suka kara fahimtar muhimmancin zaben mutanen kirki a matsayin shugabanni, musamman bisa yadda Shugaba Buhari ya sauya Najeriya cikin kankanin lokaci zai sa Buhari ya samu karin kuri’a a zaben mai zuwa.

Ibrahim Usman ya ce, “Muna da ’yan sa-kai a matakin jihohi 21 da 21 a mazabun sanatoci da 21 a kowace karamar hukuma  da 21 a mazabun unguwanni da kuma 21 a kowane akwatin zabe. A rumfunan zabe dubu 120 za mu samu adadin mutum miliyan 2 da dubu 725 da 359 na magoya bayan Buhari. “Kowanne dan kungiya daga cikin miliyan biyu din nan zai farauto masu jefa kuri’a guda 4. Saboda haka idan ka tara yawan ’yan kungiya da yawan mutane masu jefa kuri’a za ka samu sama da miliyan 40,” inji shi

Game da yadda  hakarsu za ta cimma ruwa ganin yadda babbar jam’iyyar adawa ta PDP da dan takararta Atiku suke kara matsa wa gwamnatin APC lamba, sai ya ce: “Shekara hudu muka shafe muna shiri domin mu ga an sake zabar Buhari don ya ci gaba da ayyukan gyaran Najeriya kamar yadda ya faro. Kuma a dalilin haka mun kulla kawance da wasu kananan jam’iyyu domin cimma nasarar hakan a 2019,” inji shi.