Search
Subscribe
Za mu share muku takaicin da PDP ta saka ku a Bayelsa – Oshiomole

Adams Oshiomhole

Za mu share muku takaicin da PDP ta saka ku a Bayelsa – Oshiomole

Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ce, jam’iyyarsa za ta gyara duk kura-kuran da Jam’iyyar PDP ta tafka a Jihar Bayelsa idan aka zabe ta a zaben Gwamnan Jihar da ke tafe wata mai zuwa. Oshiomole ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da yakin neman zabe na Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Ogbia da ke Jihar Bayelsa. Ya ce, jam’iyyar ta kafa kwamitin mutane masu nagarta, don haka babu abin da take jira in ban da samun nasara a zaben na 16 ga watan Nuwamba. Oshiomole ya ce “APC ta zo ne domin ta gyara kura-kuran da PDP ta yi a Jihar Bayelsa.”

Ya ce Gwamnatin APC a karkashin Dabid Lyon za ta yi aiki tukuru wajen samar da tsaro da aikin yi da bunkasa rayuwar mutanen Jihar Bayelsa. Kuma ya ce hakika Jam’iyyar APC ce za ta samu nasara a zaben Gwamnan da ke tafe, wanda zaben nata ne zai sake dawo da martabar jihar da jama’a suka rasa sakamakon rashin jagoranci mai kyau.

Har ila yau, Oshiomole ya ce, ba wai bincike ko bin diddigin gwamnatin PDP ke gabansu ba, illa gyara kura-kuran da gwamnatinsu ta tafka a jihar.

Da yake nasa jawabin, dan takarar Gwamnan na Jam’iyyar APC, Dabid Lyon ya ce, ba zai yi alkawari, kuma ya ki cikawa ba. Ya kara da cewa zai yi amfani da kyawawan kudirorin da za su kawo wa Jihar Bayelsa ci gaba. Kuma  ya ce zai farfado da katafaren kamfanin samar da wutar lantarki na Jihar Bayelsa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin