✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu wadata kasar nan da shinkafa – kungiyar RIFAN

kungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya reshen Jihar Kebbi watau (RIFAN) ta ce tana sa ran samar da shinkafa buhu miliyan biyu da ‘yan kai a…

kungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya reshen Jihar Kebbi watau (RIFAN) ta ce tana sa ran samar da shinkafa buhu miliyan biyu da ‘yan kai a kowace shekara kan tsarin da babban bankin Najeriya  (CBN) ya fito da shi. Shugaban kungiyar ta kasa reshen Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sahabi Augie, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, a lokacin da gwamnan babban bankin Nijeriya, Mista Godwin Emefiele da kuma ministan aikin gona, Audu Ogbeh suka ziyarce shi.

Shugaban kungiyar ya ce, fiye da manoma dubu 70 a kowace jiha za su shiga cikin shirin don cimma burin da aka kaddamar, ya kuma ce manoma da suke iya noma tsakanin hekta daya zuwa hudu na shinkafa za a sanya su a cikin shirin don su ma su samu damar amfani da wannan shirin. 

Alh. Muhammad Sahabi ya ce, kungiyar tasu za ta duba da kuma aiki tare da jami’an babban bankin Najeriya, bankin Aikin noma da jami’ai na Jihar Kebbi don tabbatar da nasarar wannan shirin a Jihar Kebbi. Ya kara da cewa an bada kayan aiki kamar irin su taki, irin shinkafa, maganin kwari, sinadarai da kayan aiki na ruwa ga kowane manomi don taimaka masa kan noma kowace hekta daya.

A nasa zantawa da manema labarai, shugaban kungiyar noman alkama a Jihar Kebbi, Alhaji Abdullahi Argungu, ya bayyana cewa manoma dubu 10 ne suka ci gajiyar shirin noman alkama a Jihar Kebbi. Shugaban ya koka da mummunan tsuntsaye dake addabar su wanda ya shafi amfanin gona na alkama a Jihar Kebbi.

Ya ce za a sake komawa aikin noman alkama na rani a shekaran nan mai zuwa. Haka kuma ya ce da yardar Allah yawan manoman alkama za su karu daga dubu 10 zuwa dubu 20 dan samar da karin lokaci ga manoman alkama a duk fadin Jihar Kebbi da kuma samar da kayan aikin noman alkama na zamani akan lokaci.