✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi dokar da za ta kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a Sakkwato – Kwamishina

Aminiya: Wadanne ayyuka ne ma’aikatarka ta aiwatar a shekara uku na Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal? Kwamishina: Ma’aikatarmu ta kula da lafiyar dabbobi da habaka kiwon…

Aminiya: Wadanne ayyuka ne ma’aikatarka ta aiwatar a shekara uku na Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal?

Kwamishina: Ma’aikatarmu ta kula da lafiyar dabbobi da habaka kiwon kifi dadaddiyar ma’aikata ce da ke kula da kamun kifi tana da ayyukka da shirye-shirye da take yi a duk fadin jihar nan don bunkasa lafiyar dabbobi da samar da aikin yi ga matasa, wajen dogaro da kansu. An yi wannan ne don kawo ci gaba a jihar nan, inda muka aiwatar da dimbin ayyuka kamar yadda jama’ar Sakkwato suka sani don wannan gwamnati aiki ta zo yi ba wasa ba. 


Aminiya: A halin da ake ciki asibitin kula da lafiyar dabbobi na Jihar Sakkwato ya yi kadan, bisa la’akari da yadda jihar ke bunkasa. Ko akwai wani shiri na fadada asibitin zuwa sassan jihar?

Kwamishina: Al’umma na karuwa dole bukatu su karu, yanzu muna da likitoci fiye da 100 sabanin inda aka fito, ka ga akwai bukatar fadadawa, kuma Mai girma Gwamna ya ba mu dama, an sanya na’ura ta zamani guda 20 duk mun yi wannan ne saboda kauce wa cutar dabbobi da ke iya sanya wa mutane, dole mu kiyaye lafiyar dabbobinmu don su ke iya sanya cuta ga mutane, mutane ba sa iya sanya musu cuta. Haka muna da kudirin kowace karamar hukuma mu gina asibitin, sannan a fadada wanda muke da shi, ya dace da zamani, har Mai girma Gwamna ya ba da umarnin fitar da kudi Naira miliyan 11 tun bara, duk saboda kare dabbobin daga cuta tare da ba su magani ga wanda abin ya shafa. A kan haka an fitar da wasu Naira miliyan 14 don sayen magani da sauran kayan bukatu na dabbobin a shirin matakin farko da na biyu, gwamnati na yin wadannan ne don kare lafiyar dabbobin.


Aminiya: Gwamnati ta fito da wani shiri na tallafa wa manoman kifi, amma sai aka ji shirin ya tsaya, ina aka kwana?

Kwamishina: Kifi nama ne mai tsada, haka abincinsa, to a nan muna da masu kiwon kifi na al’ada wato masunta, suna da bambanci da masu kiwon domin sana’a ta zamani ko a wurin sayarwa suna da bambanci. Mun yunkuro sosai sai aka samu karancin ruwa da wuri, ciyawra shalla ta yi yawa tana tsotse ruwa, tana kawo mana cikas. Sakkwato ba mu da ruwa kamar Kebbi, yanayin wuri yana taimaka wa sana’ar, ba mu cin kifi sosai, sannan ba ka ganinsa ana amfani da shi a makaratunmu, amma duk da haka muna kan nazarin hanyoyin taimaka musu bayan an kara tona gulabe, a samo iri a sanya a ilimantar da masu sana’ar, domin su daina faduwa a harkar, a samu hanyoyin sarrafawa na zamani don daina hasara, a kuma rika gasawa ana fitar da shi waje. Masu kiwon kifi 140 har da mata cikinsu suka amfana da shirin da muka fito da shi na karfafa wa masu sana’ar, inda muka ba su robar ruwa babba, abincin kifin da irinsa, don kawai a kara samun kifin a jihar nan, inda shirin ya lakume Naira miliyan 19. Don haka shirin bai tsaya ba, yana nan yana ci gaba.


Aminiya: Ina aka kan shirin samar da madarar shanun kasar Ajentina da fitar da nama waje da gwamnatin nan ta ce za ta yi. Wace manufa take son cimma?

Kwamishina: Manufar da muke da ita yadda ake yekuwar mutane su shiga kiwo irin na zamani, su kuma san bambancin dabbobin da muke da su kowace akwai abin da ake so gare ta, ga dashen maniyyi da ake yi, sai a samar da aikin yi ga matasa a wurin sarrafa madara da nama da sauransu sama da mutum dubu daya ne za su samu aiki a harkar kafin nan da watan biyar na bana za a bude wannan katafaren wuri a karamar Hukumar Rabah. Sannan kamfanin zai rika fitar da nama kasashen waje, an je an yi yarjejeniya da kamfanin sun aiko mana da takardar gayyata suna son Mai girma Gwamna ya je, amma  wasu uzururuka suka hana shi ya tafi, aka dage zuwan amma nan gaba kadan za a sanya lokaci ya tafi don Mai girma Gwamna babu abin da ya sanya a gaba face ci gaban Sakkwato da al’ummarta.


Aminiya: A karshe wadanne matakai kake ganin idan gwamnatin kasar nan ta dauka, zai iya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a Najeriya?

Kwamishina: Ka dubi matakin da muka dauka a jihar nan, Mai girma Gwamnan Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ba mu dukan goyon bayan da muke bukata, domin shi masanin doka ne ya san dokoki da suka shafi jinsin jama’a, wannan ya taimaka mana bisa ga tsarin da muka bi na kula da makiyaya sosai sabanin inda aka fito, makiyaya ba su samu kular da ta dace ba, manoma ne kawai ake gani bayan an manta da kiwo da noma tare suke tafiya. Kowane ba ya tafiya sai da daya. Mun yi la’akari da cewa al’umma na karuwa sannan kiwo na habaka, mashekarin shanu da burtali da mashaya ana mamaye su yanzu, hukuma za ta tsara wurin kiwo a karfafa shi wanda wannan ne aka kasa aiwatarwa har ya haifar da rigimar don manomi da makiyayi ba wanda aka ayyana wurinsa don ya tsaya kada ya shiga cikin na wani matukar ba a kula da wannan ba rigimar ba za ta kare ba. 

A nan Jihar Sakkwato za mu yi doka kan wannan don kawo sauki da kawar da rigima a tsakanin makiyayanmu da manomanmu. Gwamna ya aminta da fitar da kudi sama da Naira miliyan 8 a sayi wasu karin abincin dabbobi don a kai wuraren kiwon dabbobi na gwamnati da ke garin Dogon Daji da Kebbe da wasu mashaya wanda yin haka zai taimaka ga samun karin dabbobi da kara ba su muhimmanci. Gwamnati ta sanya hannu ga takardar yarjejeniya da masu saka hannun jari na Kudancin Amurka don samar da wata masana’anta ta dabbobi.