✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi wa Nurudden hannuwan roba – Shugaban Hukumar NYSC

Shugaban Hukumar Yi wa Kasa Hidima ta Kasa (NYSC), Birgediya-Janar Shu’aibu Ibrahim ya dauki alkawaren cewa hukumarsa za ta sama wa Nuruddeen Tahir wanda ya…

Shugaban Hukumar Yi wa Kasa Hidima ta Kasa (NYSC), Birgediya-Janar Shu’aibu Ibrahim ya dauki alkawaren cewa hukumarsa za ta sama wa Nuruddeen Tahir wanda ya rasa hannayensa biyu hannuwan roba.

Shugaban Hukumar NYSC din ya dauki wannan alkawarin ne a lokacin da ya ziyarci Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jalingo fadar Jihar Taraba inda aka kwantar da Nurudeen da wadansu masu yi wa kasa hidima da suka samu hadarin motar da ta raba Nuruddeen da hannunsa daya da ya rage.

Ya ce tuni aka soma tuntubar wasu sassa na kasashen waje da nufin sama wa Nuruddeen Tahir hannuwan roba masu inganci da za su taimaka masa ya yi rubutu da cin abinci da sauran ayyuka da masu hannu ka iya yi.

Janar Shu’aibu Ibrahim ya ce bayan haka za a bai wa Nurudden aikin yi kai-tsaye tare da tabbatar da cewa an samar masa da dukkan abubuwan da za su taimaka masa ya samu saukin tafiyar da rayuwarsa.

Shugaban ya kuma bayyana cewa babban nanufar hukumar ita ce ta inganta jin dadin matasa masu yi wa kasa hidima saboda haka wannan matashi Nuruddeen wanda dan asalin Jihar Kano ne ya nuna kishin kasa duk da kasancewar hannu daya yake da shi kafin hadarin ya sa ya sake rasa daya hannunsa.

Nuruddeen Tahir a kwance a gadun asibiti
Nuruddeen Tahir a kwance a gadun asibiti

Ya ce hukumar a Jihar Taraba bayan kammala horon da ake bai wa sababbin masu yi wa kasa hidima ta tausaya masa inda ta nemi ya koma jiharsa ta Kano don gudanar da aikinsa amma ya ce shi a Jihar Taraba kuma a yankin tsaunin Mambilla zai gudanar da aikinsa. Ya ce sai kuma ga shi ya samu hadarin mota ya rutsa da shi inda ya sake rasa hannunsa daya saboda haka ya zama wajibi a taimaka masa ta kowace fuska don ya samu saukin rayuwa.